Ku San Malamanku tare da Sheikh Tijjani Bala Kalarawi
Latsa hoton da ke sama ku kalli bidiyon:
Fitaccen malamin addini Sheikh Tijjani Bala Ƙalarawi ya ce gwagwarmayar neman ilimi ta haɗa shi da manyan malaman ɓangarorin Musulunci a Najeriya Shiekh Abubakar Mahmud Gumi da kuma Dahiru Usman Bauchi.
Shehin malamin ya faɗa wa BBC Hausa haka ne ta cikin Ku San Malamanku, inda ya ce ya san 'yan boko da sarakuna sanadiyyar Abubakar Gumi yayin da ya san manyan malamai a wajen Sheikh Isiyaka Rabi'u da Mahmudu Salga.
An haifi Shiekh Tijjani Bala a shekarar 1947 (shekara 75) a unguwar Fagge da ke birnin Kano.
Malamin ya shafe mafi yawan rayuwarsa ta zama da karatu a Kano.
Neman ilimi

Asalin hoton, Family
Sheikh Tijjani Bala ya fara karatun allo a birnin Kano a wajen Malam Musa Wahu. Kazalika ya yi karatu a Maikwaru da kuma makarantar Haido.
Sai dai malamin ya ce bai yi karatun boko ba a farkon rayuwarsa saboda ɗabi'ar malamin da zai koyar da su ta fitsari a tsaye.
"A wannan lokaci, wani da aka kawo zai koyar da boko sai ya yi fitsari a tsaye a gindin wata bishiya. Sai mahaifinmu ya gani ya ce 'ba da ni ba'," in ji shi. Amma daga baya ya yi karatun boko a Jos na Jihar Filato.
Daga cikin malamnsa akwai Tijjani Zangon Barebari da Ustazu Adamu Najume da Malam Hamza.
Tsakanin ɗariƙa da Izala

Asalin hoton, Family
Malam ya ce ya yi mu'amala da manyan malaman ɗariƙa da kuma na Izala a lokacin da ya bar Kano zuwa wajen Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
"Lokacin da nake zuwa wajen Abubakar Gumi, shi yana ɓangaren 'yan boko da sarakuna, su kuma Sheikh Umaru Sanda da Awwal Sirajo da Zubairu Sirajo suna ɓangaren ɗariƙa da malaman sufaye. To sai ya zamana ina tsakaninsu."
Shiekh Gumi ya bai wa Tijjani Bala shawarar ya nemi Sheikh Ahmadu Arabi idan ya je Jos yawon wa'azi, wanda shi ne Alƙalin Alƙalai na jihohin Filato da Binuwai, inda ya haɗu da malamai irinsu Ibrahim Musaddadu da Ali Ɗan-Takai da Malam Ƙawwasu.
Kazalika, Gumi ya ba shi shawarar cewa duk inda ya je ya saka littafi karatun da ya tarar ana yi a wajen.
A irin wannan hali ne ya haɗu da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda yake zuwa wajen wa'azinsa kuma ya rufe taro da addu'a.
'Alaƙata da Malam Lawan Ƙalarawi'
Ainahin sunan malamin shi ne Tijjani Bala, kafin daga baya Ƙalarawi - sunan Malam Lawan Ƙalarawi - ya ƙaru a sunansa.
Lawan Ƙalarawi fitaccen malami ne a Kano. Alaƙar malamn biyu ita ce surukuta.
Malam Lawan yana auren 'yar uwar Tiijani Bala shaƙiƙiya.
'Buhari da IBB ɗalibaina ne'

Asalin hoton, Family
Sheikh Tijjani Bala ya ce majalisar karatun tafsirinsa na 'Yan Bahed ta kai shekara 38 "wadda ke da almajirai manya".
"Daga cikin almajiran akwai Birgeidya Janar A.A. da Janar Buhari da Janar Babangida da Janar Abdulsalami, tun sun 'yan ƙananan hafsoshi," a cewar shehin malamin.
Ya ƙara da cewa da yawan ɗaliban da ke karatu a Jami'ar Bayero na zuwa makarantar ɗaukar karatu.











