Cinikin kifi, husufin wata da ƙaunar Putin a cikin hotunan Afirka na mako: 13-19 Mayun 2022

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna daga nahiyar Afirka na da kuma na wasu ƴan nahiyar a wasu wuraren a duniya a wannan makon.

Short presentational grey line
Men in traditional attires attend the first 'Great bekoji run' running event, in Bekoji, Ethiopia, on May 15, 2022. - Bekoji, a town 225 kms (139 miles) south of Addis Ababa is renowned for producing running phenoms who have collectively got 22 Olympic medals

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Garin Bekoji da ke ƙasar Habasha ya shahara wajen samar da manyan waɗanda suka iya gudu a duniya kuma a ranar Lahadi mutane sun fito don murnar ƙaddamar da gagarumin gudu na Bekoji.
Semakaleng Mathebula, South Africa"s first Black female hot-air balloon pilot releases propane gas in preparation for take off in Johannesburg, South Africa, May 15, 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Afirka ta Kudu ma a ranar Lahadi, Semakaleng Mathebula, ƴar ƙasar baƙar fata ta farko matuƙiyar jirgin balam-balam tana shirin tashi a jirgin daga birnin Johannesburg.
Charlie Cavanagh (red) of Canada competes with Ichrak Chaib (blue) of Algeria in the 66 kg match of the International Boxing Association (IBA) Women's World Boxing Championships in Istanbul, Turkiye on May 18, 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ichrak Chaib ƴar Algeria daga hagu ta dambata da Charlie Cavanagh daga dama a Canada a wani wasan dab da na ƙarshe a gasar damben boxing ta duniya a Turkiyya eranar Laraba.
May 13, 2022 Tunisia"s Ons Jabeur signs autographs for fans after winning her quarter final match against Greece"s Maria Sakkari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Babban dan wasan tennis na nahiyar Afirka dan kasar Tunusiya Ons Jabeur, ya tsaya don gaisawa da masoyansa bayan wani wasa da aka yi na bude gasar Italiya a ranar Juma'a.
Hailu Biniam Girmay of Eritrea and Team Intermarché - Wanty - Gobert Matériaux celebrates at finish line as stage winner ahead of Mathieu Van Der Poel of Netherlands and Team Alpecin - Fenix during the 105th Giro d'Italia 2022, Stage 10 a 196km stage from Pescara to Jesi 95m / #Giro / #WorldTour / on May 17, 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Biniam Girmay ɗan Eritrea ya kaffa tarihi a ranar Talata a yayin da yake dab da yin nasara a ƙarshen mataki na 10 na gasar Giro D'Italia. Ya zamo ɗan Afirka baƙar fata na farko da ya yi nasara a gasar tseren kekuna.
Kenyan activists from the Social Justice Centres Working Group, shout slogans and hold placards during a People's March against the high cost of living in the streets of Nairobi, Kenya, 17 May 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƙaruwar farashin kayayyki na shafar ɗumbin mutane a faɗin nahiyar inda a ranar Talata a Nairobi babban birnin Kenya, masu fafutuka suka yi zanga-zanga a gaban majalisar dokoki don taimakon marasa ƙarfi.
A supporter of Malian Interim President wears a face mask of the President of Russia, Vladimir Putin, during a pro-Junta and pro-Russia rally in Bamako on May 13, 2022. - Several hundred Malians have gathered in Bamako to support the junta, the army and military cooperation with the Russians

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A franar Juma'a kuwa a Mali, wani magoyin bayan gwamnatin mulkin soja a ƙasar da kuma Shugaba Outin, ya ɗauki hoto tare da wani mutum da ya saka fuskar Putin, a lokacin da mutane ke kai komo a kan titunan Bamako, babban birnin ƙasar.
A Jewish pilgrim prays at the Ghriba synagogue in Tunisia's southern resort island of Djerba on May 18, 2022 during the annual Jewish pilgrimage to the synagogue. - May 18 marks the beginning of of the annual pilgrimage of Jews to the oldest Jewish monument built in Africa, after a two-year absence due to Covid-19.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mata na addu'a a wani tsohon wajen ibada na Yahudawa a nahiyar da ke garin Djerba.
Farmers harvest wheat to increase local wheat production in order to fill the wheat shortage in the country in Al Minufiyah, one of the important grain production centers of Egypt on May 14, 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani manomi a Masar ya loda kayan girbi a kansa, wanda ya girbe ranar Asabar.
A Rwandan model with disability wearing Karssh Collections, walks on the runway during the Isano fashion show at Century Park, Kigali, Rwanda on May 17, 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wani mai tallan kayan ƙawa a Uganda mai lalurar gani ya bayyana a wajen taron tallan kayan ƙawa a birnin Kigali, yana nuna damuwar da mutane masu naƙasa da ƴan luwaɗi da madigo ke ciki.
A model wearing Miss Warma designers clothes walks on the runway during a street fashion show in the popular neighbourhood of Dapoya as part of Ouaga Fashion Week 2022, in Ouagadougou, late May 14, 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar da daddare kuwa aka yi taron Kayan Kawa na Ouaga a babban birnin Burkina Faso inda mutane suka yi cincinrindo suna kallo.
A customer speaks with a fish seller at Mile 12 International Food market in Lagos, Nigeria May 13, 2022

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar a wata kasuwar abinci a Lagos da ke Nigeria, wani mai saye da kuma mai sayar da kifi suna ciniki a kan farashi.
The supermoon lunar eclipse as seen from the Zambezi River in Zimbabwe. In this year"s only full lunar eclipse, the moon will turn a deep coppery red as it drifts into the shadow of the Earth. The Earth"s atmosphere then bends light from the sun and bathes the moon in a red hue. Issue date: Monday May 16, 2022

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, An yi husufin wata a duniya - kuma wannan hoton an dauke shi ne da tsakar darem Litinin daga kogin Zambezi a Zimbabwe.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka