Ku San Malamanku tare da Malam Garba Tudun Wada Gombe

An wallafa

Malam Garba Tudun Wada a Gombe haifaffen jihar Sokoto ne kuma a can ya taso, daga baya ya koma Gombe inda ya yi karatunsa da kuma harkokin da'awa da wa'azi.

Ya fara karatu tun daga na farfaru da babbaƙu a wajen wani malami, Malam Buba na makarantar allo. Bayan nan kuma ya yi "saukar zuƙu" daga nan ya yi karatu a wajen Malam Muhammadu Basakkwace.

Bayan da ya koma Gombe ya kafa makarantar koyar da yara alkurani. A duk lokacin da malam Basakkwace ba ya nan malam Garba ke koyar da yara, amma a lokacin da yake nan to shi ma yana daga cikin masu koyo, in ji shi.

Ya ce an shafe shekaru ana tafe har makarnta ta ɗaukaka ta faɗaɗa. "A haka ilimina ya bunƙasa har na zama cikakken malami a makarantar."

Ana tafe a haka har ya kasance yana wakiltar Malam Basakkwace a al'amura da yawa.

Ya ce yau shekara takwas kenan da rasuwar Malam Basakkwace shi ya karɓi ragamar makarantar wacce ke da ɗalibai daga Balanga da Billiri da Bajoga da Dadin Kowa wato Yamaltu Deba da Dukku.

A dalilin da'awa akwai wurare masu nisa ma da na shiga da ƙafa da suke ce min ba su taɓa jin ma labarin Al-ƙur'ani ba.

"Na taba zuwa wani gari muka je masallaci da asuba na same shi maƙil, amma sarkin ya ce min dalilin wa'azin da taba zuwa na yi musu ne ya sa suke zuwa sallar asuba.

"Akwai inda na je wa'azi suka ce tun wa'azin da na je na musu shekara goma baya suna amfani da shi sosai. Hakan ya sa na kan ji daɗi sosai."

Wasu na baya da za ku so ku karanta

Malam ya ce a cikin surorin Al-ƙur'ani ya fi shan wahala a haddar Suratu Mudaffidin.

A ƙasashen da ya taba zuwa kuwa ya ce daga Saudiyya sai Sudan sai Chadi. Sannan ya je Umra da Hajji sau bakwai.

Sannan ya ce a nan gaba yana son zuwa ƙasar Syriya don ya ga ƙaburburan wasu annabawa da ke can.

A ɓangaren abinci kuwa Malam ya ce ya fi son abin da ya shafi amsara da shinkafa, sai kuma miyar kuka.

Malam yana da mata huɗu da ƴaƴa 42 da da jikoki 55.

Babban burinsa shi ne ya ga addinin Musulunci na tafiya ana kuma karanta Al-ƙur'ani.

Sannan yana burin ya ga duk Musulmi ya samu kyakkyawan ƙarshe da gamawa lafiya.

Malam ya ce a tambayoyi kuwa an fi yi masa tambaya a kan matsayin addinin Musulunci.