Shereen Abu Aqleh: 'Sojojin Isra'ila sun kashe' ƴar jaridar Al Jazeera a wani samame

Journalists react next to the body of Al Jazeera correspondent Shireen Abu Aqleh, who was shot dead during an Israeli raid in the occupied West Bank city of Jenin (11 May 2022)

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An harbi Shereen Abu Aqleh duk da cewa tana sanye da hular kwano da rigar kariya a cewar Qatar
An wallafa

An harbe wata gogaggiyar ƴar jaridar Al Jazeera Shereen Abu Aqleh a yayin da take bayar da rahoto kan wani samame da dakarun sojin Isra'ila suka kai a birnin Jenin da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Kafar yaɗa labaran mai cibiya a ƙasar Qatar ta ce sojojin Isra'ila ne suka harbe ƴar jaridar mai shekara 51 "da gangan" kuma "ba tare da ta yi wani abu ba. Sannan an ji wa wani ɗan jaridar raunuka sakamakon harbinsa da aka yi.

Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ƙaryata cewa dakarunta kan ƴan jaridar suka kai hari.

Suna nuna yiwuwar "wataƙila ƴan bindigar Falasɗinu ne" suka kashe ta a yayin da ake musayar wuta.

Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Yair Lapid ya bayyana mutuwar Shereen a matsayin "abin takaici" ya kuma ce an ƙaddamar da binciken haɗin gwiwa tsakanin ƙasarsa da hukumomin Falasɗinu.

Ya ƙara da cewa: "Dole ne a dinga bai wa ƴan jarida kariya a yankunan da ake yaƙi kuma dole ne dukkanmu mu ɗauki alhakin gano gaskiyar abin da ya faru."

Mataimakiyar Ministan Harkokin Wajen Qatar Lolwah al-Khater ta ce, "a fuska aka harbi Shereen Abu Aqleh" duk da cewa tana sanye da hular kwano da rigar kariya.

Shereen Abu Aqleh

Asalin hoton, Al Jazeera

Bayanan hoto, Shereen Abu Aqleh ta shafe shekara 15 tana aiki a matsayin ƴar jaridar da ke ba da rahotanni kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu

Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu ce ta tabbatar da mutuwar Abu Aqleh inda ta ce an yi gaggawar kai ta asibiti a cikin wani mummunan yanayi bayan harbin nata.

Shereen Abu Aqleh fitacciyar ƴar jaridar sashen Larabci na Al Jazeera ce, wacce ta shafe shekara 15 tana aiki a matsayin mai bayar da rahotanni kan rikicin Isra'ila da Falasdinu.

Wata ƴar jaridar ta Al Jazeera Nida Ibrahim ta ce Shareen "ƴar jarida ce da ake girmamawa sosai" kuma labarin rasuwarta ya kaɗa ƴan jarida da dama da suke aiki da ita."

Rikice-rikicen da ke ta faruwa a makonnin baya-bayan nan tsakanin Larabawa ƴan Isra'ila da ita Isra'ilar sun yi sanadin mutuwar Isra'ilawa 17 da wasu ƴan Ukraine biyu.

A ƙalla Falasɗinawa 26 aka kashe - da suka haɗa da masu kai hare-hare ko sojoji ko kuma fararen hula a lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Isra'ila ta fi mayar da hankalin aiwatar da ayyukanta ne a gundumar Jenin, yankin da Falasɗinawa huɗun da suka kai hare-hare kan Isra'ilar suka fito.