Ku San Malamanku tare da Malam Aliyu Hammari Walama
An haifi Malam Aliyu Hammari a cikin garin Gombe a watan Satumba 1984, a nan kuma jihar ya fara karatun addinin musulunci a wajen kakansa Sarkin Malamai Abubakar Baffa wanda ya dade da rasuwa, nan ya yi karatun Al-Kur'ani da wasu littafan Fiqhu.
A hannun kakan nasa ya yi karatun littafan Kawa'idi da Ahlari kamar matakin nazire kenan, daga nan aka kai su makarantar da 'ya'yan kowa ke zuwa, wato makarantar Alhaji Umaru Tudun Wada da ke cikin garin Gombe, wajen Alaramma Yakubu Bara a nan suka sauke Al-Kur'ani mai tsarki.
Daga nan shi ma ya ce ya kamata su matsa wata makarantar da ta fi wadda yake koyar da su, ya ba su zabin makarantu guda uku;
- Makarantar Modibbo Idirisa
- Makarantar Modibbo Abu Waile Kole
- Makarantar Malam Gidado
Daga bisani aka daidaita kan su tafi makarantar Malam Abu Waile Kole, a hannunsa ya yi kashi 70 cikin 100 na littafa addini, wasu karance-karancen na da'awa da wa'azi a wajen Malam Muhammadu Basakkwace ya yi. Bangaren Tafsir wajen Murshid Usman Baba Liman da Malam Dahiru Isa Bolari.
A bangaren karatun boko ya yi karatun firamaren a makarantar Karangara a cikin Gombe da karamar sakandare makarantar Pilot, sai babbar sakandare da ya yi a makarantar kimiyya da fasaha ta Gombe, sai ya yi Difloma a makarantar Legal inda ya karanci fannin Shari'a, daga nan jami'ar Maiduguri ya karanta Shari'a and Public Law, sai makarantar koyon aikin Lauya a Yola da ke jihar Adamawa.
A shekarar 2019 aka tabbatar da shi a matsayin Lauya, ya sake komawa jami'ar Maiduguri inda ya ke yin digiri na biyu duk dai a fannin shari'a.
Malam Aliyu ya ce baya ga kasar Saudiyya ya na fatan kai ziyara wasu kasashen da suka shafi aikin lauyanci, saboda ana amfani da dokokin Birtaniya, don haka burinsa ya je kasar Birtaniya inda zai gano ainahin tushen inda aka kafa dokokin da ake amfani Najeriya.
Malamin ya ce ya sha wuya a bangaren karatun Alkurani saboda hadda ake son yi, shi kuma ba inda ya ba shi wuya kenan. ''Akwai bambanci sosai da koyarwar lokacinmu, domin mun sha bulala idan muka gagara ba da hadda amma duk da hakan, Alhamdulillah saboda mun yi karatu mai inganci. Sai kuma lokacin da muna makarantar koyon aikin Lauya, akwai abin da ake kira Presentaion, wato tsayawa gaban mutane ka yi bayani a kan wani maudu'i da aka bukaci ku yi bincike a kai, nan ma na sha wuya domin kusan kullum sai an yi. Lokacin da aka sanar da cewa na tsallake wannan siradin ba karamin farin ciki na yi ba,'' in ji Malamin.
Malam Aliyu Hammari ya ce ya na jin dadin karanta Suratu Maryam, har ta kai ya na yawan karatanta a matsayin karatun sallah, sannan ta dauki hankalinsa saboda tattaro addinai guda biyu, wato addinin Musulunci da na Kirista.











