Shanghai lockdown: Yadda masu kai saƙo a Shanghai ke shan baƙar-wuya

An wallafa

Kwanaki da dama da aka shafe a cikin dokar kulle a Shanghai, mutum miliyan 25 da ke zaune a birnin sun ci gaba da dogara ne kan masu kai saƙo da babura domin samun kayan abinci.

Sai dai masu irin wannan aikin na kai saƙo waɗanda adadinsu ya kai mutum 200,000 sun fuskanci ƙalubale da dama da suka haɗa da na muhalli da kuma tsaron lafiyarsu. Wasu masu aikin kai saƙo sun shaida wa BBC labarinsu.

Ina cikin hidima, mutane da dama na buƙatar kayayyaki. Ina shafe rana ina kai saƙonni, idan na ga alamar ƙarfe 12:00 na dare, ina samun wani wuri na ɗan fake domin na yi bacci.

Na bar gidana tun a ranar 8 ga watan Afrilu kuma ban koma ba tun lokacin. Gwamnatin Shanghai na barin masu aikin kai saƙonni shiga da barin gidajensu.

Sai dai duk da haka wasu gidajen kan saka tsare-tsarensu inda akasarinsu ba su barin masu aikin kai saƙonni komawa gidajensu idan sun fita.

Akwai otel-otel da dama waɗanda ke a buɗe, amma ba kowaɗanne bane ake bari muna shiga.

Akwai wani tanti da ke a gaban gidana irin waɗanda ake sakawa a wuraren da ake gudanar da riga-kafin korona. A lokacin da na bar gida, masu kula da harkokin gidan suka buƙace ni da na taimaka na sawo musu wasu kayayyaki inda a maimakon haka za su bari na kwana a tantin da ke waje da dare. Sai na bar duka kayana a wurin.

Sai wata rana aka wayi gari babu tantin. Na kasa gano inda kayayyakina suke. Masu kula da gidan sai suka ce mani lamarin bai shafe su ba. Haka ma masu gadin gidan suka ce mani ba su san inda kayayyakina suke ba.

Hakan ya sa dole na nemi wani sabon wuri domin ci gaba da kwana. Kwana a ƙarƙashin gada ba wani sabon abu bane ga mu masu aikin kai saƙonni - hakan na bamu kariya daga iska da kuma ruwan sama. Na kan yi bacci nan take bayan na kwanta - Ina matuƙar gajiya a lokacin!

Sai wata rana ban kula da hasashen yanayi ba. Ana zabga ruwa mai ƙarfin gaske kuma karƙashin gada a cike take da jama'a. Daga baya sai na samu wani ɗakin ATM domin na kwana. Wurin yana da daɗin kwanciya saboda babu kowa a wurin. Fargabar da nake yi ita ce kawai kada ƴan sanda su zo su fatattake ni.

Amma bayan shafe dare biyu a wurin, da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ƴan sandan da ke shawagi sun ganni inda suka kore ni. Sun shaida mani cewa na tafi wuraren da ake kula da waɗanda ba su da muhalli. Na yi ƙoƙarin haka amma wurin ba a buɗe yake ba, ko masu gadi babu.

Tun da farko taliya ce nake ci kullum. Sai dai daga baya wani rukuninmu na masu kai saƙonni mun gano wani wurin cin abinci da aka buɗe shi cikin sirri da ake zuwa a sawo abinci.

Yan sanda sun basar sun yi kamar ba su san da wurin ba. Muna buƙatar wurin cin abinci ƙo. Haka kuma wasu shaguna suna da soket na lantarki a waje. Muna lallaɓawa domin mu caza wayoyinmu.

Akwai wani labari da ake yaɗawa cewa wani mai kai saƙonni ya yi hatsari ya rasu. Ina damuwa kan hakan zai iya faruwa da ni amma ina taka tsan-tsan. Ina tafiya a hakali. Idan na yi hatsari a wajen gari, abin zai ƙazanta sosai.

Babban tashin hankalin shi ne idan babur ɗin mutum ya lalace babu wurin da mutum zai kai gyara, mutum ba zai iya ci gaba da aiki ba.

Mutane da dama sun karanta labarai da ke cewa masu aikin kai saƙonni za su iya samun yuan 10,000 a rana, kimanin dala 1,500. Tun bayan lokacin ne mutane da dama suke ta tambayata kan yadda za su zama masu kai saƙo.

Shawarar da nake ba mutane ita ce, "kada ka zama ɗan kai saƙo".

A Shanghai, kuɗin da muke samu a matsayin masu kai saƙonni ba laifi. Amma akasarin masu kai saƙonni suna samun kuɗaɗe kaɗan ne a duk rana. Kuma bana tunanin kowa ne zai iya jure irin wannan wahalar.

Amma kuma kun san idan ba mu yin haka, babu wata ribar da za mu samu ko da a lokacin dokar kulle ne. Abu ne mai wahala.

An haife ni a shekarar 1999 a lardin Anhui. A lokacin da na kammala makarantar sakandire, ban samu damar shiga jami'a mai kyau ba sakamakon kuɗin ya yi tsada matuƙa ga iyayena. Ba ni da shekaru masu yawa kuma ban san me zan yi ba. Mahaifiyata sai ta bani shawarar na je wurin ɗan uwana a Shanghai. Aƙalla dai ba zan rasa wurin kwana ba ko kuma na rasa abinci.

Sai na zo Shanghai domin gudanar da aiki tare da ɗan uwana da kuma sayar da kwamfuta. Na shafe shekara biyu ina wannan aikin. Ba kasuwa a lokacin korona, hakan ya sa na nemi wani aiki.

Ban da wurin zama a lokacin, sai na samu wani ɗakin haya wanda sama da mutum guda ke zama inda na rinƙa zama da wani mai kai saƙonni. Da alama yana samun kuɗaɗe da dama.

Sai na mashi magana na ce mashi ɗan uwa, za ka iya taimaka mani nima na soma wannan aikin? Kimanin wata shida da suka wuce sai na soma wannan aikin.

Mutane sun shaida mani cewa Shanghai birni ne da aka samu ci gaba matuƙa, fiye da garin da na fito. Amma ko a yanzu ƴan uwana na ta neman na koma gida. Duk sun ji labarin halin da ake ciki. Abin mamaki ne a halin yanzu da har mutane za su zauna da yunwa a Shanghai.

Ba wai ina cikin yunwa bane, amma asali ni daga ƙauye na fito, har a garken shanu na kwana a lokacin ina ƙarami.

Ina samun aƙalla yuan 4.5 a duk kai saƙo. Amma a yanzu na daina irin wannan aikin saboda kuɗin sun yi kaɗan, babu mai irin wannan aikin a yanzu. A yanzu ina aikin kai saƙo ne na zaman kaina inda nake chattin da mutane domin karɓa ko kai saƙo, kuma ina samun kusan yaun 1,000 a duk rana.

Ina ganin manyan gidaje da ke sayen abinci a ƙungiyance sai dai ƙananan gidaje waɗanda ke da gwamman mutane ba su da komai. Abu ne mai wahala su samu a kai musu kayayyaki, abu ne mai wahala kai saƙonni a irin waɗannan wurare. Dattawan mutane da dama a wannan lokacin ba su san yadda za su gama kai domin sayen kayayyaki ba.

Waɗanda ke bayar da odar ƙananan kayayyaki ba su samu a kai musu abubuwan su a yanzu. Shagunan sayar da kayan marmari sun daina sayar wa mutum ɗaya tilo - dole ne sai dai a saya da yawa.

Idan wani na son kayan lambu na kimanin yuan 20, sai na shafe aƙalla rabin yini ina nema kuma ba lallai na samu ba, sakamakon ana sayar da kayayyaki ne da yawa kawai na sama da yuan 100.

A yanzu ba mu da abinci kuma ba mu da ruwa haka kuma muna zama a kan tituna ne. Na san aƙalla masu aikin kai saƙonni aƙalla 40 da ke cikin halin da nake.

Akwai masu aikin kai saƙonni waɗanda ke yi wa kamfanoni aiki kuma kamfanonin na basu ɗakuna a otel. Sai dai akwai wasu waɗanda ke samu oda daga kwastamomi kamar mu, kuma ƙaramar hukuma ba ta yi komai ba domin samar mana da wuraren da za mu zauna.

Gidan da anek zaune a ciki ba za su yarda na koma can ba, inda suka ce akwai yiwuwar zan dawo musu da wannan annobar. Ko da na yi gwajin korona kuma gwaji ya nuna cewa ba na ɗauke da cutar, ba za su bari na shiga ba.

Ina yawan zuwa asibitoci domin a yi mani gwaji a kullum. Ina tsoron kamuwa da cutar korona - duka masu irin wannan aikin na irin wannan tsoron.

Ina neman wuri ne kawai na kwanta a waje. Ƙafa ta na wuri, mutum zai iya shaƙar warin tun daga nesa! zan yi wanka ba da daɗewa ba, watakila bayan an ɗage dokar kulle.