Yadda Amurka ta gayyaci China 'cin abincin rana'

An wallafa

Akwai abubuwa biyu da suka faru a ƙarshen 2001 da suka girgiza duniya.

Duniya ta mayar da hankali kan harin 9/11. Amma bayan watanni uku, wato a ranar 11 ga watan Disamba, Hukumar kasuwanci ta Duniya WTO, ta kasance a tsakiyar wani taron da zai yi tasiri sosai a ƙarni na 21, wanda zai sauya rayuwar mutane da dama a duniya fiye da hare-haren da aka kai a Amurka.

Amma kaɗan ne suka san hakan ta faru balantana ma ranar. Shigar da kasar China a hukumar kasuwanci ta duniya, ta sauya duk wata hamayya ga Amurka daTurai da galibin ƙasashen Asiya, da ma duk wata ƙasa da ke tunƙaho da masana'antu, kamar mai da karafa.

Wannan wani abu ne da ba mayar da hankali akai ba a siyasar duniya da tattalin arziki. Shi ne tushen rikicin rikicin matsalar kuɗi.

Alƙawalin da irinsu tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya bayar shi ne "shigo da daɓiu na dimokuradiyya da ƴancin tattalin arziki," zai ba ƙasar da ta fi yawan al'umma a duniya damar samun ƴanci ita ma na siyasa.

"Idan mutane suna da ƙarfi ba wai kawai mafarki ba, amma tabbatar da burinsu, za su iya buƙatar a ji buƙatunsu," in ji shi.

Amma wannan tsarin ya gaza. China ta fara jan ragama na matsayinta na yanzu a matsayin ta biyu mai ƙarfin tattalin arziki a duniya - tana kan hanyar zama wadda ta fi ƙarfin tattalin arzikin duniya.

Wakiliyar Amurka da ke tattauna yarjejeniya da China ta hukumar kasuwanci ta Duniya Charlene Barshefsky, ta faɗa wa wani taron kungiyar kasuwanci a Washington a wannan makon cewa tsarin tatttalin arzikin China "wanda ba a amince ba" ƙasashen yammaci na ganin "ba ka iya samun al'umma mai kirƙira ace kuma akwai ikon siyasa"

Ta ƙara da cewa, "Ba wai cewar an inganta karfin kirkire-kirkire na ƙasar China ta hanyar tsarin tattalin arzikinta ba." "Amma ana cewar abin da kasashen Yamma ke tunanin tsarin da bai dace ba yana iya zama ba haka ba."

Har zuwa 2000 rawar da China ke taka ga tattalin arzikin duniya ya zama ɗaya daga cikin mafi ƙarfin masana'antu roba. Yana da muhimmanci amma ba wani sauyi a duniya.

Kasancewar China a jerin manyan ƙasashe masu masana'antu ya ba da haifar da samun gagarumin sauyi a duniya.

Karfin yawan ma'aikatan China da manyan masana'antu na fasahar zamani da alaƙa ta musamman tsakanin gwamnatin China da kamfanonin ƙasashen yammacin duniya sun samar da sauyi a duniya.

Yawan ma'aikata na China sun fara kera kayayyakin da ke da nasaba da na yammacin duniya, yayin da China ta shigar da kanta wajen samar da kayayyaki na manyan kamfanoni na duniya ke samarwa.

Shigar da China cikin tattalin arzikin duniya ya samu gagarumin nasarori a fannin tattalin arziki, ciki har da kawar da matsanancin talauci, wanda ya kai miliyan 500 kafin zama mamba ta Hukumar kasuwanci ta WTO.

Kuɗaɗen ajiyar ƙasar ya ƙaru da kaso 15 zuwa tiriliyan 2.3 yayin da duniya ke ciniki daga hukumomin kuɗi na China.

A 2000, China ce ta bakwai da ke fitar da kayayyaki a duniya, amma cikin sauri ta karɓe matsayi na farko. Ci gaban China a shekara ya kai kashi 8, kuma ya ƙaru zuwa kashi 14 har zuwa 15 a bara.

Jiragen dakon kaya sun kasance tushe na kasuwancin duniya.

Cikin shekara biyar bayan China ta shiga Hukumar kasuwanci ta Duniya WTO, yawan kwantaina a jirgin ruwa da ke shiga China ya ƙaru daga miliyan 40 zuwa sama da miliyan 80.

Daga 2011, shekara 10 bayan ta zama mamba a WTO, yawan kwantena ya lullunka zuwa miliyan 129.

A bara yawan ya kai kwantaina miliyan 243, kuma kusan rabin waɗanda ke shiga China ba komi a cikinsu, kusan kuma duk waɗanda ake fita da su a cike suke da kayayyaki.

An faɗada ayyuka na hanyoyi a China daga kilomita 4,7000 a 1997 zuwa 161,000 a 2020, wanda ya zama mafi girma a duniya da ke haɗa kashi 99 na birane da ke da yawan jama'a 200,000.

A 2005 China ta karon farko ta fara fitar da ƙarafa kuma tun daga lokacin ta zama wadda ta fi fitar da ƙarafa a duniya.

Zuwa 1990, karafan da China ke samarwa sun kai ton miliyan 100 a shekara, bayan zama mamban WTO, ya matuƙar ƙaru zuwa miliyan 700 a 2020 yayin da ya zarta biliyan ɗaya a 2020.

China yanzu tana samar da kashi 57 na ƙarafa a duniya fiye da wanda suaran sassan duniya ke samarwa a 2001. Haka ma sauran abubuwan da masana'antu ke samarwa.

A kasuwancin kayayyakin da ke amfani da lantarki da na katako, China ta zam kan gaba inda ta tilasta faɗuwar farashi a faɗin duniya.

Masana sun lura da yadda farashin ya yi ƙasa bayan chigar China WTO. Tufafin da China ke fitarwa ya lunka daga 2000 zuwa 2005, kuma darajar a kasuwar duniya ta cira daga matsayi na kashi ɗata cikin biyar zuwa ɗaya cikin uku.

Bayan 2005, an ɗage ƙayyade abubuwan da aka ba China damar fitarwa a kasuwancin tufafi wanda ya bunƙasa kasuwancin na China.

Sai dai yayin da kayayyakin China ke ƙara tsada, samar da kayayyakin ya karkata zuwa ƙasashe masu tasowa kamar Bangladesh da Vietnam ya sauka zuwa kashi 32 na tufafi a bara.

Ministan China na da ya jagoranci shigar ƙasar WTO Long Yongtu, ya yi bayani kan abubuwan da suka faru a tsawon shekara 20. "Ban yarda cewa shigar China WTO wani kuskure ne (ga Amurka da ƙasashen Yammaci)," in ji shi.

A cewarsa "abin da ke faruwa shi ne idan China ta samu ci gabanta, za ta samarwar sauran duniya kasuwa babba."

Ya ce siyasar Amurka ce ta kasa magance tasirin hamayyar China a wasu ɓangarori.

"Ganin laifin wasu ba ya da wahala, amma ban yi tunanin ganin laifin wasu zai iya magance matsala ba. Idan da ba China, wasu masana'antun Amurka za su koma ne Mexico."

China ta samu nasarorinta na tattalin arziki a WTO.

Yanzu haka Biden ba ya son yin gaggawar sauya wasu manufofi na waɗanda ya gada. Fargabar cinikayya gaskiya ce. China ta yi amfani da WTO ta zarta matsayinta.

Misali ta yi ƙoƙari wajen wajen tsara abubuwan da za su taimakawa masa wajen sauya tattalin arzikin da zai yi daidai sauyin yanayi.

Ta yi tsari na faɗaɗa masana'antunta a sassan duniya. Amurka na dina yadda za ta tafi da China ta hanyar diflomasiyya da tattalin arziki da kuma neman ƙawance a wannan manufar a Turai da Asiya.

Don haka shekaru 20 da suka gabata - wani mataki ya sauya duniya. Babban nasara ce ga China. Tsarin siyasa na ƙasashen yammaci bai yi nasara. Kuma maimakon China ta zama kamar ƙasashen yammaci a siyasance sakamakon wannan matakin, ƙasashen yammaci a fuskar tattalin arziki suna neman zama kamar China.