Eid al-fitr: Hotunan yadda aka yi karamar Sallah a fadin duniya

An wallafa

A ranar Litinin ne akasarin Musulmai a fadin duniya suka yi Sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadan.

Mun zabo muku hotuna yadda aka gudanar da bukukuwan Sallah a sassa daban-daban na duniya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun miliyoyin 'yan kasar wajen yin sallah karama a Abuja, babban birnin kasar...

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun miliyoyin 'yan kasar wajen yin sallah karama a Abuja, babban birnin kasar...
Bayan an sauko daga sallah, sai shugaban kasar ya karbi baki samu yi masa gaisuwar Sallah, kuma ya dauki hotuna da iyalai da manyan jami'an gwamnati.

Asalin hoton, Nigeria Pressidency

Bayanan hoto, Bayan an sauko daga sallah, sai shugaban kasar ya karbi baki samu yi masa gaisuwar Sallah, kuma ya dauki hotuna da iyalai da manyan jami'an gwamnati.
A birnin Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya halarci sallar idi tare da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran jama'a
Bayanan hoto, A birnin Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya halarci sallar idi tare da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran jama'a
A Kaduna ma, Gwamna Nasir El-rufai ne ya halarci idi wanda tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya jagoranta.

Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna

Bayanan hoto, A Kaduna ma, Gwamna Nasir El-rufai ne ya halarci idi wanda tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ya jagoranta.
A jihar Katsina an yi hawan sallah karon farko cikin shekaru uku
Bayanan hoto, A jihar Katsina an yi hawan sallah karon farko cikin shekaru uku
Su ma al'ummar birnin Malang na kasar Indonesiya sun yi tasu sallar Idi a yau Lininin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Su ma al'ummar birnin Malang na kasar Indonesiya sun yi tasu sallar Idi a yau Lininin
Yadda Musulmai suka gudanar da Sallah a birnin London

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda Musulmai suka gudanar da Sallah a birnin London