Guguwa a Iraƙi: An hana jiragen sama tashi a Baghadaza da Najaf yayin da sararin samaniya ya sauya kala

Guguwar kura

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan daya gabata an samu faruwar guguwar kura makamacin wannan a Irakin
An wallafa

An samu wata gagarumar guguwa da ke tafe da kura, wadda ta sauya sarararin samaniya da hana zirga-zirgar jiragen sama a Iraki.

Gajimaren kurar ya sauya sararin samaniya zuwa ruwan lemo yayin da guguwar ta auka wa sassan kasar.

An dakatar da tashin jiragen sama na Bagadaza da Najaf saboda rashin kyawun yanayi. Ana sa ran za a ci gaba da samun yanayi irin wannan har zuwa ranar Litinin, in ji masu hasashen yanayi.

Irin wannan guguwar ta zama ruwan-dare gama gari a yankin Gabas ta Tsakiya, inda masana ke zargin sauyin yanayi da rashin sarrafa filaye da kuma karancin ruwa ne suka haddasa ta.

A wasu wurare a Iraki a ranar Asabar, an iyakance ganuwa zuwa kasa da mita 500.

Ko a watan da ya gabata sai da Iraki ta fuskanci irin wannan gaguwa, inda mutane da dama sun bukaci magani a asibiti saboda matsalar numfashi

Yadda ake samun karuwar yawan guguwa tafe da kura a Gabas ta Tsakiya

Dan sandan Iraki

Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Bayanan hoto, Wani jami'in dan sanda na ba motoci hannu a birnin Bagadaza
Iraki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iraki na fuskantar karancin ruwan sama

A baya ofishin kula da yanayi na kasar Iraki ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mai yiwuwa kasar za ta kara fuskantar guguwa da ke turnuke ko ina da matsanancin kura, saboda fari da kwararowar hamada da kuma raguwar ruwan sama.

Rashin wuraren masu launin kore a cikin birane da kewaye kuma na iya haifar da matsalar.

A 2016, Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) ta yi hasashen cewa Iraki za ta iya ganin lamuran da suka shafi kura har 300 a cikin shekara guda nan da 2026.

Iraki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A watan Nuwamba, bankin duniya ya ce Iraki na iya fuskantar raguwar albarkatun ruwa da kashi 20% nan da shekara ta 2050

A watan Nuwamba, bankin duniya ya ce Iraki na iya fuskantar raguwar albarkatun ruwa da kashi 20 cikin 100 nan da shekara ta 2050.

Iraki

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto, Guguar kura kan haifar matsalar numfashi da ciwon zuciya a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya

Guguwar tafe da kura kan haifar da matsalar numfashi da ciwon zuciya a cewar hukumar lafiya ta duniya .

Garin Najaf

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najaf