Guguwa a Iraƙi: An hana jiragen sama tashi a Baghadaza da Najaf yayin da sararin samaniya ya sauya kala

An wallafa

An samu wata gagarumar guguwa da ke tafe da kura, wadda ta sauya sarararin samaniya da hana zirga-zirgar jiragen sama a Iraki.

Gajimaren kurar ya sauya sararin samaniya zuwa ruwan lemo yayin da guguwar ta auka wa sassan kasar.

An dakatar da tashin jiragen sama na Bagadaza da Najaf saboda rashin kyawun yanayi. Ana sa ran za a ci gaba da samun yanayi irin wannan har zuwa ranar Litinin, in ji masu hasashen yanayi.

Irin wannan guguwar ta zama ruwan-dare gama gari a yankin Gabas ta Tsakiya, inda masana ke zargin sauyin yanayi da rashin sarrafa filaye da kuma karancin ruwa ne suka haddasa ta.

A wasu wurare a Iraki a ranar Asabar, an iyakance ganuwa zuwa kasa da mita 500.

Ko a watan da ya gabata sai da Iraki ta fuskanci irin wannan gaguwa, inda mutane da dama sun bukaci magani a asibiti saboda matsalar numfashi

Yadda ake samun karuwar yawan guguwa tafe da kura a Gabas ta Tsakiya

A baya ofishin kula da yanayi na kasar Iraki ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mai yiwuwa kasar za ta kara fuskantar guguwa da ke turnuke ko ina da matsanancin kura, saboda fari da kwararowar hamada da kuma raguwar ruwan sama.

Rashin wuraren masu launin kore a cikin birane da kewaye kuma na iya haifar da matsalar.

A 2016, Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) ta yi hasashen cewa Iraki za ta iya ganin lamuran da suka shafi kura har 300 a cikin shekara guda nan da 2026.

A watan Nuwamba, bankin duniya ya ce Iraki na iya fuskantar raguwar albarkatun ruwa da kashi 20 cikin 100 nan da shekara ta 2050.

Guguwar tafe da kura kan haifar da matsalar numfashi da ciwon zuciya a cewar hukumar lafiya ta duniya .