Yajin aikin ASUU: Ana ce-ce-ku-ce kan sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa na karamin ministan ilimi a APC

Wata ƙungiya da ake kira Project Nigeria Group, PNG ce ta ce ta saya wa ƙaramin ministan na ilimi fom na takarar shugaban ƙasa

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Wata ƙungiya da ake kira Project Nigeria Group, PNG ce ta ce ta saya wa ƙaramin ministan na ilimi fom na takarar shugaban ƙasa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya na ce-ce-ku-ce kan batutuwan da suka shafi yajin aikin ƙungiyar malaman jami'oi ta ASUU.

Sayen fom na takarar shugaban ƙasa da rahotanni suka ce ƙaramin ministan ilimi Hon Chukwuemeka Nwajiuba ya yi a jam'iyyar APC ya fi jan hankali, yayin da har yanzu gawamnatin tarayya ba ta sasanta da ƙungiyar malaman jami'o'i ba ta ASUU.

Tun ƙayyade farashin fom na takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC kan naira miliyan 100, batun ke ci gaba da jan hankali a Najeriya.

Wata ƙungiya da ake kira Project Nigeria Group, PNG ce ta ce ta saya wa ƙaramin ministan na ilimi fom na takarar shugaban ƙasa. Amma ƴan Najeriya hankalinsu ya fi karkata ga ministan.

Wannan kuma na zuwa bayan an kasa samun fahimtar juna tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyar ASUU.

Ƴan Najeriyar kuma na tattaunawa kan sanarwar da Jami'ar Jihar Kaduna KASU ta fitar kan ranar komawa koratu, wanda ke nuna bijerewa yajin aikin ƙungiyar ASUU da ta shafe fiye da wata biyu tana yajin aiki.

ASUU na cikin batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya a ranar Laraba, inda aka ambaci ASUU fiye da sau 40,000 a Twitter.

Me ƴan Najeriya ke cewa

Yawancin ƴan Najeriyar na tsokaci ne kan takarar shugaban ƙasa da ƙaramin ministan na ilimi ke yi bayan kasa magance yajin aikin ASUU tsawon lokaci.

Wasu kuma sun fi mayar da hankali ne kan yawan kuɗin sayen fom na takarar shugaban ƙasa naira miliyan 100.

Wani mai amfani da shafin Twitter @FS_Yusuf_ tambaya ya yi cewa: "ta yaya za a ce ASUU na yajin aiki kuma ministan ilimi ya sayi fom naira miliyan 100 don takarar shugaban ƙasa. wannan wace irin ƙasa ce?

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

@KefasKyenmann ya ce: "mutum nawa ya san ƙaramin ministan ilimi? ya sayi fom na takarar shugaban ƙasa. Yana son zama shugaban ƙasa! amma a wani ɓangaren ga ASUU har yanzu na yajin aiki, dukkanin jami'o'in tarayya a rufe.

@Ijogbonofunilag ya wallafa sako tare da mau'du'in a kawo ƙarshen yajin aikin ASUU, yana cewa: "Jami'o'i a rufe saboda yajin aiki amma ga ƙaramin ministan ilimi yana fifita takarar shugaban kasa ba tare ya sauka daga kujerarsa ga waɗanda za su iya sasantawa da ASUU"

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wasu ƴan Najeriyar kuma na tattaunawa ne kan sanarwar da Jami'ar jihar Kaduna KASU ta fitar inda ta sanar da ranar 9 ga watan Mayu a matsayin ranar komawa kakar karatu na 2020/2021.

Sanarwar na ɗauke da sa hannun Sakataren Jami'ar Abdullahi Zuru inda yake umartar ɗalibai da malaman jami'ar su dawo karatu.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wasu na ganin sanarwar ta Jami'ar jihar Kaduna na nufin wani mataki da ke nuna jami'oin jihohi za su bijerewa ASUU.

@Abubaka46737620 ya ce: abin da ya kamata su yi kenan

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Twitter

Asalin hoton, Twitter

@Ashibuoguh ta yi tambaya ne: Ko me ya jami'oin jihohi suka shiga yajin aikin ƙungiyar malaman jami'oin tarayya. Shin gwamnatin tarayya ce ke kula da jami'oin jihohi?

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Sai dai a ra'ayin @ZeroXjs yana ganin wasu na ganin duk jami'o'in da suka fice daga yajin aikin ASUU za su fuskanci matsalolinsu ne su kaɗai. Zamanin ƙarin kudin makaranta na tafe.

Twitter

Asalin hoton, Twitter