SpaceX: Shin za a iya samar da nama a sararin samaniya?

A stock image of an astronaut eating a hamburger

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga James Clayton
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan fasaha a arewacin Amurka
  • An wallafa

Jeff Bezos da Elon Musk dukkaninsu na son su mulki sararin samaniya. A yayin da ita kuma hukumar Nasa ke kokarin saka mutane kan doron duniyar Mars mai kura.

Amma idan mutane na son kafa wata al'umma a kan duniyar wata ko duniyoyi, me za su ci?

An gudanar da bincike da dama don gano ko tsirrai za su iya rayuwa a sararin samaniya.

Kuma a makon da ya gabata, an fara gudanar da gwaji don gano ko kwayoyin halittar nama za su iya yaduwa.

Wani matakin farko ne na gwajin yiwuwar samun abinci mai gina jiki, wani babban ci gaba - akalla burin masu bincike - kan makomar bulaguron sararin samaniya.

Gidan gona na Aleph Farms na kasar Isra'ila ne ya shahara wajen noman nama daga kwayoyin halitta, shi ne ya bullo da wannan bincike, kuma tawagar 'yan sama-jannati ta mai zaman kanta ta farko da ta fara ziyartar hukumar lura da sararin samaniya ta kasa da kasa.

Ko da yake masu nuna shakku sun bayyana cewa wannan hanya ba mai dorewa ba ce ga 'yan sama-jannatin da za su dogara da ita - ana cewa noman nama ba zai taba zama abu mafi sauki fiye da kai shi can daga doron kasa ba.

Yadda ake samar da nama

Noman nama da kwayoyin halitta - musamman a wani ma'auni - ko a doron duniyar kasa ba mai sauki ba ne. Gidan gonar Aleph Farms daya daga cikin kamfanoni da dama ne da suka yi kokarin samar da ''naman da kirkiro'' amma shi ne na farko da ya yi kokarin yin shi a sararin samaniya.

Kamfanin ba ya son yin amfani da kalmomi na "naman da aka samar a dakin bincike" - amma kuma a zahiri ko kusa hanyar noman sa ba ta yi kama da na noma da kiwon da aka sani ba.

Ana bai wa kwayoyin halittar shanu (koda yake zai iya zama a ko wace irin dabba) abubuwa da suke bukata don su girma ko su yadu, kamar su na'ukan sinadarai da abinci kamar amino acids da carbohydrates.

Kwayoyin halittar kan yadu har sai sun zama kamar fata, wanda daga karshe su zama naman da za mu iya ci. Wannan hanya ana kiranta da "noma" ko "yaduwa".

An bunkasa naman a cikin tankuna da ke kama da abin da ka ke gani a masana'antar sarrafa barasa fiye da a ce wata gona.

An tsallake daukacin matakan rayuwar dabbar da ake kiwo don samun nama daga - haihuwa, rayuwa da kuma yanka.

A steak grown by Aleph Farms

Asalin hoton, Aleph Farms

Bayanan hoto, Naman da gidan gona na Aleph Farm ya kirkiro

Masu nuna goyo baya na cewa wannan hanyar na da alamun yin amfani ga muhalli, alal misali na rage yawan fitar da gurbatacciyar iskar methane.

Shin mene ne dalilin bunkasa nama a sararin samaniya?

Zvika Tamari, wanda ke jagorantar shirin sararin samaniyar na kamfanin na Aleph Farms, ya bayyana cewa masana kimiyya ba su san ko shin za a iya maimaita wannan hanya a wuri marar nauyi ko maganadisu ba.

"Mun san daga binciken kimiyyar da aka gudanar a baya cewa kimiyyar halittar jiki da kimiyyar dabbobi na yin dabi'a daban a muhalli wanda ba shi da nauyi ko maganadisu … don haka, takamaimai ba mu sani ba, babu wanda ya sani, idan wadannan hanyoyi na noman yaduwar nama kan faru a sararin samaniya.''

A ranar 8 ga watan Afrilu ne mutane hudu suka kusa cikin sararin samaniya a cikin kumbon kamfanin jigilar sararin samaniya ta SpaceX, a zuwan su na farko zuwa na Tashar sararin samaniya ta kasa da kasa, sun zo da wani akwati mai girman kwalin takalmi dauke da kwayoyin halittar dabbobi - da duk wani abu da suke bukata don girma.

An tura Larry Connor da Eytan Stibbe da kuma Mark Pathy daga cibiyar lura da sararin samaniya ta Kennedy Space Center a jihar Florida, tare da tsohon da sama jannati Michael Lopez-Alegria.

An sa ran dawowarsu sararin samaniya a ranar Lahadi 24 ga watan Afrilu, bayan an yi wa kwayoyin halittar binciken kwakwaf.

Amma shin ya dace a yi hakan?

Koda gwajin ya samu nasara kuma aka tabbatar da cewa za a iya noman nama a sararin samaniya, ba lallai ne yana nufin abu ne mai kyau ba.

Akwai dalilan da suka saka ba a saka naman da aka noma daga kwayoyin halitta a manyan shuguna ba. Ko shakka babu, duk da cewa daruruwan miliyoyin daloli ne aka saka a cikin masana'antar.

Har yanzu kamfanin Aleph Farm na jiran amincewar hukuma a kasar Isra'ila kafin a yi amfani da shi a gidajen cin abinci.

Wannan abinci ne wanda bai kafa kan sa a duniya ba a doron kasa, ballantana a sararin samaniya.

Akwai sauran karin wasu matsalolin idan aka zo batun noman nama a sararin samaniya. Na farko shi ne batun haihuwa.

"Kwayoyin halittar dabba na girma a hankali.'' In ji David Humbird, wani injiniyan kimiyyar sinadarai a Berkeley.

"Muddin kayoyin cutar bacteriya ko fungus suka shiga cikin kwayoyin halitta za su yadu cikin sauri daga kwayoyin halittar dabba kuma zai maye gurbi, don haka ba za ka iya sake hada kwayoyin halittar ba.

Kuma hada kwayoyin cutar bacteriya. Kuma dole ka jefar da shi," in ji Mista Humbird.

Aleph Farms ya ce ya yi amanna cewa za a iya shawo kan matsalar haihuwa, musamman a sararin samaniya inda ake bukatar samar da adadin nama kadan. Amma kuma gurbacewa za ta yi matukar muni ga al'ummar duniyar Mars.

Aleph Farms rendering of what a farm on Mars could look like

Asalin hoton, Aleph Farms

Bayanan hoto, Shin naman da aka kirkira a dakin bincike zai iya taimakawa wajen shawo kan matsalar sauyin-yanayi?

Aleph Farms ya kuma bayyana cewa daukar abinci zuwa sarari samaniya na da matukar tsada. Alkalumma na bambanta sosai, amma kuma kididdigar hukumar Nasa daga shekarar 2008 ta nuna dala 10,000 kwatankwacin fan dubu bakwai.

"Duniyar Mars na da nisan miliyoyi da milyoyin kilomita. Don haka kafin samar da abincinka daga gida, babbar dam ace'', in ji Mista Tamari.

Karen Nyberg tsohuwar dan sama jannati ne a hukumar Nasa wanda ya shafe watanni biyar da rabi a tashar lura da sararin samaniya, kana yanzu a kan kwamitin bayar da shawarwari na Aleph Farms ne.

Ta bayyana cewa abinci na taka muhimmiyar rawa a yanayin lafiyar kwakwalwar 'yan tawagar,

"Abinci na zuwa ne a cikin wadannan fararen jakunkunan da dole sai mun rika saka wa ruwa, kamar su madarar gari da sauransu … Ina kwadayin jin kamshin soyaiyiyar tafarnuwa da man zaitun, wani abu ne da bamu da shi. Don haka duk abinda za mu iya samu mu dawo da shi gida ina abu ne mai kyau."

Mis Nyberg, na da yakinin sabon abinci da ganyaye na da muhimmanci idan ana sa ran mutane za su kasance a nesa da doron duniya na tsawon shekaru.

Lallai ne, muddin a shirye ake wajen tura mutane zuwa duniyar Mars, sanin yadda za a ciyar da 'yan sama jannati abinci mai gina jiki da ba zai lalace ba - kana da dandano mai dadi - yana da matukar muhimmancin kana da sarkakiya.

Aleph Farms na da buri mai yawa, amma nuna cewa za a iya samar da nama da wani adadi a doron duniya wata babbar ayar tambay ace ga kamfanin