Maigari Dingyadi: Muna daukar matakan kyautata walwalar 'yan sandan Najeriya

An wallafa

Ma'aikatar harkokin 'yan sanda ta Najeriya ta ce tana ɗaukar matakai domin kyautata walwalar 'yan sandan ƙasar, musamman wajen inganta albashinsu dama basu kariyar da ta dace.

Ministan harkokin 'yan sanda a Najeriyar, Muhammad Maigari Dingyaɗi, ya shaida wa BBC cewa a matsayinsu na shugabanni suna daukar matakai da dama na ganin cewa sun hana aukuwar abubuwan da ke samun 'yan sanda a kasar.

Ya ce "Na farko dai muna kyautata kayan aikinmu, domin idan dan sanda ya fita aiki da kayan aiki na gari, to ana ganin in sha Allahu zai fi samun dawowa lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba".

Ministan ya ce a yanzu za su kyautata kayan aiki, sannan dangane da batun albashi kuwa, ana nan ana kokari wajen ganin an aiwatar da fara biyan sabon albashi kamar yadda shugaban Najeriya ya yi alkawari.

Muhammad Maigari Dingyadi, ya ce in sha Allah nan bada jimawa ba kowanne dan sanda zai samu albashin da ya kamata ace ya samu.

A baya-bayan nan ne aka yi ta yaɗa raɗe-raɗin cewa ƙananan 'yan sandan ƙasar za su tsunduma yajin aiki saboda rashin biyansu sabon albashin da shugaban kasa ya yi alƙawarin ƙara musu.

To amma ministan harkokin 'yan sandan, ya musanta cewa za su tafi yajin aiki, in da ya ce maganar sam ba gaskiya bace.

Karin bayani

Jami'an 'yan sanda a Najeriya dai, sune mafi kusanci ga jama'a wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu a duk in da suke.

To amma a wasu lokuta a kan samu akasin haka, a maimakon su kare rayukan su sai a cutarsu, wannan kuwa na da nasaba da rashin kayan aiki na gari.

Kazalika karancin albashin da ake basu ma, na jefa su cikin mawuyacin yanayi, in da za kaga wasunsu na karbar albashin da bai taka kara ya karya ba, abin da ake zargin cewa hakan shi ke tilasta musu karbar na goro a wajen jama'a.

Bisa la'akari da halin da 'yan sandan ke ciki ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin kara musu albashi da kuma smaar musu da kayan aikin da ya dace don samu rinka aikinsu yadda yakamata.