Ba za mu sa dokar ta baci kan sha'anin tsaro ba a Najeriya - Ministan 'Yan sanda

An wallafa

Ministan Lamurran 'yan sanda na Najeriya Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce babu buƙatar sanya dokar ta ɓaci kan sha'anin tsaro a ƙasar.

Minista Dingyadi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis, inda yake amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa gwamnati ta yanke hukuncin yi wa ƴan sandan ƙasar ƙarin albashi.

Ƴan Najeriya sun daɗe suna kiraye-kirayen a sanya dokar ta ɓaci a jihohi musamman na yankin arewa maso yamma, duba da halin taɓarɓarewar tsaro da yankin ke ciki na hare-haren ƴan bindiga da satar mutane.

Ya ce duk da cewa Najeriya ƙasar dimokradiyya ce kuma kowa na da damar faɗin albarkacin bakinsa, "amma dai mu ba mu da shirin sanya dokar ta ɓaci a kasar nan kan waɗannan matsaloli."

"Ko ka sa dokar ta ɓaci ko ba ka sa ba abin da ake so shi ne a samu sakamako. Wurare da dama kan sa dokar ta ɓaci a fannoni da dama kamar sha'anin ilimi, amma sai ka ga babu wani bambanci."

"Da a saka dokar ta ɓaci da ba a saka ba duk abin da ake yi shi za a yi, wanda ake iya yi ma shi za a yi," kamar yadda Minista DIngyadi ya faɗa," in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi ayyukan da suka dace ba tare da ta saka dokar ta ɓaci ba.

"To ka sa dokar ta ɓaci ka ƙuntatawa wasu ina ga hakan bai yi ba. A dai ga abin da ake son a yi. kuma In Shaa Allahu za mu yi ayyukan da suka dace ba tare da mun saka dokar ta ɓaci ba," in ji shi.

Ya kuma amsa tambayar da aka yi masa cewa ko matsalolin tsaron ƙasar sun fi ƙrfin ƴn sanda ne shi ya sa ake kawo sojoji suke yi?

Sai ya ce: "Ƴan sanda ne kan gaba wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa, amma a yanzu saboda yawan abin, shi yasa jami'an tsaro daga sauran fannoni suke shiga lamarin."

Abin da ya sa aka ƙarawa ƴan sanda albashi

A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ƴan sandan kasar sabbin kuɗaɗen alawus waɗanda za su sa albashin da suke ɗauka ya ƙaru da kashi 20 cikin 100.

Ministan Lamurran ƴan sanda na kasar Muhammadu Maigari Dingyadi ne ya sanar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron majalisar zartarwar kasar mako-mako.

A cewar ministan na lamurran 'yansanda, za a fara biyan wannan sabon tsarin biyan alawun na musanmman wanda majalisar zartarwa ta amince da shi ne a watan janairun 2022; wato watan gobe kenan.

Ya shaida wa BBC cewa manufar ɗaukar matakin a daidai wannan lokaci shi ne gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Buhari na ƙoƙarin kyautata ayyukan ƴan sanda don su samu gudanar da ayyukansu musamman a wannan yanayi da ake ciki a kasar.

"Idan kana son ɗan sanda kuwa ya gudanar da aikinsa, to wajibi ne ka kula da shi ka kyautata rayuwarsa da ta iyalansa don ya samu ƙwarin gwiwar tunkarar matsalolin tsaro da muke fama da su," in ji shi.

Wasu ƴan ƙasar na ganin a baya an sha yin irin waɗannan ƙare-ƙaren albashin amma ba a ga tasirin da hakan ke yi ba.

Sai dai Minista Dingyaɗi ya ce an dade ba a yi wa yan sanda ƙarin albashi ba. "Kuma ina tabbatar da cewa a yanzu da aka samu ƙare-ƙaren, na tabbata kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

To ko ƙarin zai taimaka wa ƴan sandan magance matsalolin da suke ciki musamman na kukan da suka daɗe suna yi kan ƙarancin albashi, wanda hakan ne ya sa ake zarginsu da karɓar na goro a bakin aiki?

Sai ministan ya ce "Baya ga ƙarin da aka yi musu, yanzu gwamnati ta ce a daina cire kashi takwas na haraji da ake cire musu a albashinsu.

"Za a dinga tara musu wannan kuɗi a wani asusu na musamman don biya musu wasu abubuwa. Sannan baya ga harajin, akwai kuma kuɗaɗen hayar gidaje."

Ministan lamurran ƴan sandan a ce za a sanya wannan ƙrin albashi a kasafin kudin kasar.

Ya kuma jaddada cewa ko shakka babu ƴan sanda suna taka rawar gani don shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

"Kuma in Allah Ya yarda da yake ana ci gaba da samun kayayyakin aiki da kuma wannan tallafi na ƙarin albashi da sauran abubuwa da ƙarin kayan aiki da za a ba su, to ina ganin za a samu ci gaba."