Ku san Malamanku tare da Malam Muhammadu Kobuwa a Gombe
An haifi malamin a wani gari da ake kira Jollo a Karamar Hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya.
Ya soma karatu a hannun mahaifinsa mai suna Muhammadu, wanda bai dade da fara karatun ba Allah ya yi masa rasuwa, inda daga nan ne kawunsa da ake kira malam Kawu ya dauko shi zuwa jihar Gombe makwabciya a wani kauye da ake kira Wuro Kachalla.
"Daga garin Wuro Kachalla ne muka taso muka dawo wani gari da ake kira garin Bappa Ibrahima inda na yi saukar karatuna a hannun kawun nawa," in ji Malamin.
"Sannan na karanta su Kurdafi, da Ashmawi, da Risala da kuma Iziyya a hannun wani malami a nan garin Bappa Ibrahima ana ce masa malam Adamu Yaro".
Daga nan kuma bayan ya je garin Malam Inna sai ya dawo cikin garin Gombe wurin wani malami da ake kira Malam Musa wani Sufi ya cigaba da karatun.
Daga nan ne ya koma wajen Shehu Manzo, amma bayan tafiyar Malam Shehu Manzo zuwa garin Khaulak na kasar Senegal sai malamin ya koma karatu garin Misa una jihar Bauchi wurin wani malami da ake kira Malam Saleh.
Bayan zaman karatun na lokaci kadan a hannun malam Saleh a garin na Misau ne kuma malamin ya koma garin Kano wurin wani malami da ake kira Modibbo Jar Kasa a inda akwai wani malami da yake musu bita da ake kira malam Mai Agogo.
Malam Muhammadu ya kuma bayyana cewa ya yi karatu a wajen malam Shehu Mai Hula a garin na Kano.

Abubuwan farin cikin da bakin ciki da malamin ba zai manta da su ba
Malam Muhammadu ya kuma shaida wa BBC cewa akwai abinda farin cikin da ba zai manta da shi ba lokacin da ya karbi darikar Tijjaniyya, da kuma lokacin da aka ba shi izinin bayar da darikar, wanda ya yi farin ciki kwarai da gaske.
Ta wani gefen kuma ya bayyana abubuwan bakin ciki da ya ce ba zai taba mantawa da shi a rayuwarsa ba.
"Rasuwar Shehu manzo ta girgiza ni, na yi bakin ciki kwarai da gaske," ya ce.
Malam Muhammadu ya kuma bayyana irin kasashen da ya je neman karin ilimin addinin musulunci da haduwa da manyan malamai da suka hada da kasar Senegal.
"Na je kasashen Burkina Faso, da Senegal, da Kamaru, da Mali da kuma Nijar, na kuma je kasar Saudi Arabia yin aiki hajji sau biyu, da kuma Umra sai shida".
Malamin yana da mata uku da 'yaya sama da ashirin, kana ta fannin abinci ya bayyana cewa yana duk abinda ya samu yana so.
Babban burin malamin
Babban burin malamin in ji shi yana son samun abinda zai yi wa bayin Allah hidima da kuma cikawa da Imani.
"Ina so in zamanto ni Musulmi ne hakika, ni mumini ne hakika, muhusini ne hakika".

Yadda malamin ya karbi darikar Tijjaniyya
Malam Muhammadu ya karbi darikar Tijjaniyya a hannun Shehu Manzo ne, kuma ya yi tarbiyya a hannun wani malami a garin Kano da ake kira malam Umaru.
Bayan Shehu Manzo ya bani izinin bayar da darika in ji malamin, ya kuma bas hi izinin bai waw ani darika.
Duk da cewa Shehu Manzo ba shi ya haifi malamin ba, amma ya samu khalifancin sa, malamin ya bayyana yadda aka yi hakan ta faru da cewa bayan rasuwar shi ne sai aka ce ɗansa mai suna Malam Yaya ya rike wannan ragamar khalifancin amma ya zamana lokacin yana aikin gwamnati ne shi yasa aka nada shi.
"Saboda khalifanci aiki ne zaunanne shi yasa sai wani Alhaji Damauri ya ce dama idan Shehu baya nan nine nake jagorancin sallah da bude wazifa, saboda haka sai Sheik Dahiru Modibbo Zailani, da Modibbo Tukur da Alhaji Ali Gombe suka amince a nada ni," in ji Malam Muhammadu.
Malamin ya kuma ce ya cigaba da dorewar dangantakarsa da zumunci da gidan Shehu Manzo a kan cewa su 'yau nwansa ne kuma 'yaya ne na jiki da kuma ruhi, shi kuma da ne na ruhi, duk abinda zai yi yana neman shawararsu.













