Kotu ta daure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan aikata saɓo

An wallafa

Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa Mubarak Bala hukuncin shekara 24 a gidan yari kan laifin ɓatanci ga addinin Islama.

An yanke masa hukunci ne kan laifuka 18 da aka zarge shi ciki har da amsa laifin aikata saɓo da ya yi a gaban kotu.

Sai dai ya shaida wa kotun cewa lokacin da ya yi rubutu bai san cewar saƙon zai iya haifar da tashin hankali ba, sannan kuma hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.

An kama Mubarak Bala, shugaban kungiyar waɗanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna.

Sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.

Sakon da ya wallafa ya fusata al'ummar Musulmai a Najeriya.

Abin da ya faru a kotun

An fara ne da karanta wa Mubarak Bala tuhuma 14 da ake yi masa kan zargin saɓo.

Sai dai ya amsa aikata kusan laifi shida daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa. Kana aka ci gaba da karanto masa laifukan nasa.

Ana karanta masa saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook da ya yi kalaman ɓatanci ga addinin Musulunci.

Ya amsa dukkan laifukansa kan dukkan tuhume-tuhume 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata.

An bai wa lauyan Mubarak minti 15 saboda ya samu damar ganawa da wanda ake ƙara.

Bayan an koma zaman kotun ne sai lauyan ya sanar da kotu cewar wanda yake karewa zai sauya amsar da ya bai wa kotun.

Sai dai ana tsaka da tattaunawa ne sai Mubarak Bala ya sanar da kotu cewar ba zai sauya abin da ya faɗa da farko ba, saboda haka ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Alkali ya tambaye shi ko ya san girman laifukan da ake zarginsa da yi da irin hukuncin da za a iya yanke masa? Sai Mubarak ya ce ya sani.

Ya ce babu wanda ya tursasa shi don ya amsa dukkan laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Sannan babu wanda ya yi masa alkawari, ko ya sanya masa wani ra'ayi, amma ya buƙaci kotu ta yi masa saussauci da kuma adalci.

Laifukan da ake zarginsa da aikatawa sun ci karo da sashe na 210 na kundun panel code.

Kotu ta same shi da laifin, sai dai ya ce a lokacin da ya yi rubutu bai san cewar zai rubutun ka iya tayar da hankali ba.

Ya ƙara da cewa hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.

Hukuncin da aka yanke masa na nufin zai zauna a gidan yari na tsawon sherkara 24.

Laifin da Mubarak Bala ya aikata

Tun a watan Afrilun 2020 ne aka zargi Mubarak Bala da cin zarafin addinin Musulunci a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Wata tawagar lauyoyi ce ta miƙa wa 'yan sanda ƙorafi a Jihar Kano inda su kuma ƴan sandan Jihar Kaduna suka kama Mubarak suka mayar da shi Kano jiharsa ta haihuwa, inda a can ne dimbin Musulamai suka rubuta wa hukumomi korafi da zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A lokacin wasu masu rajin kare hakki sun yi ca a shafukansu na zumunta suna neman a saki Mubarak Bala, wadanda suka ce yana da 'yancin shiga addinin da ya kwanta masa a rai.

Barista Salisu Salisu Umar ne jagoran lauyoyin da suka yi ƙorafi kan Mubarak, kuma tun farko ya faɗa wa BBC cewa ba don ya bar addinin Musulunci suka nemi a kama shi ba.

"Mun yi musu ƙorafi ne kan aibata Annabi S.A.W. da ya yi a shafinsa na Facebook," a cewar Salisu Salisu.

Ya ci gaba da cewa: "Ba wai don ya yi ridda ba ne ko sabo, korafinmu a kan barin masu addini su yi addini ne."

"Abin da muke nufi shi ne, tun da shi (Mubarak Bala) ya bar Musulunci tun a shekarar 2014 bai kamata kuma ya rika aibata addinin ba da kuma abin da masu binsa suka yi imani da shi.

"A matsayinmu na lauyoyi, daga cikin hakkinmu mun nemi 'yan sanda su binciki abin da yake fada ko ya saba da abin da aka iyakancewa mutum ya yi magana kan addini."

Barista Salisu ya bayyana cewa suna so ne a hukunta shi da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Wane ne Mubaraka Bala?

Mubarak Bala shi ne shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya wato Humainists Asociation of Nigeria.

A shekarar 2014 ne matashi Mubarak Bala mai shekara 29, a lokacin, da ke birnin Kano ya ce bai yarda da samuwar Allah ba kuma ya ce ya bar addinin Musulunci.

Iyayensa sun kai shi asibitin masu tabin hankali domin binciken lafiyarsa a lokacin.

Sai dai ya samu ya riƙa yada halin da ya shiga ga duniya ta shafinsa na twitter ta hanyar amfani da wata waya da aka kai masa a sace a asibitin.

Abin da ya ja hankalin wata kungiya mai da'awar kare hakkin wadanda ba su da addini mai suna International Humanist and Ethical Union, wadda ta shiga kiran a sake shi.