PRP ta ce a shirye take ta yi gogayya da manyan jam'iyyun Najeriya a zabe mai zuwa

An wallafa

Jam'iyyar PRP mai ikirarin ta talakawa ce a Najeriya, ta ce a shirye take ta kara da manyan jam'iyyun siyasar kasar a zabe mai zuwa.

PRP, wadda ta gudanar da babban taronta a ranar Asabar, ta ce yanzu ta fara shiri don tunkarar zabuka masu zuwa.

Falalu Bello, shi ne shugaban jam'iyyar na kasa, ya kuma shaida wa BBC cewa, a yanzu za su zauna domin fitar da 'yan takara a dukkan jihohin Najeriya.

Ya ce, bisa la'akari da cewa jam'iyyarsu ta PRP, ita ce ta fi dukkan jam'iyyun siyasa a Najeriya dadewa, dole su fitar da 'yan takarar da za suyi wa talakawa aiki.

Shugaban jam'iyyar ta PRP, ya ce in banda APC da PDP, babu wata jam'iyya da ta kafa gwamnati a Najeriya sai jam'iyyarsu ta PRP.

Ya ce, "Mun yi gwamnati a tsohuwar Jihar Kaduna da tsohuwar Jihar Kano, kuma jama'a sun ga abin da muka yi, jam'iyyace ta talaka, kuma har yanzu a Jihar Kaduna ba a yi gwamnatin da ta yi wa talakawa aiki kamar PRP ba.

Shi ma tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, wanda dan jam'iyyar ne, ya shaida wa BBC cewa, su a PRP abin da suka sanya a gaba shi ne a zabi mutanen kirki a sa su shugabanci, domin al'umma ta amfan.''

Farfesa Jega, ya ce " Irin tabargazar da muke gani ana yi da sunan shugabanci a Najeriya, gaskiya idan har aka ci gaba a haka to za su durkusar da kasar."

Tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriyar, ya ce dole a samu a ceto talaka kana a biya masa bukatunsa, a kawo tsaro da sauran abubuwan da suka dace wadanda za su inganta rayuwar al'umma.

Ya ce," Don haka jam'iyyarmu za ta dukufa wajen tabbatar da cewa wadannan zabuka da za a yi mun tsaida mutanen kirki, kuma sun ci zabe domin a inganta al'amura na zabe a kasarmu."

Farfesa Jega, ya ce za su zo da tsari dalla-dalla wanda zai nuna muhimman abubuwan da ya kamata a fara da su idan sun ci zabe.

Ya ce, a shekarar 1979, da PRP ta ci zabe a wasu jihohin Najeriya, mutane sun gani domin sai da ta cika dukkan alkawuran da ta dauka.

Karin bayani

A ranar Asabar ne jam'iyyar PRP ta gudanar da babban taronta na kasa a Abuja babban birnin tarrayar Najeriya.

A yayin taron an yi gyara a kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Jam'iyyar ta kasance mafi dadewa a cikin jam'iyyun Najeriya a yanzu, kuma jam'iyyar na ikirarin cewa ita ce jam'iyyar talakawa a Najeriya.