Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na gudanar da babban taronta

An wallafa

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya na gudanar da babban taronta na kasa, inda wakilai daga sassan kasar za su zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin jam`iyyar nan da shekara huɗu masu zuwa.

Mutum tara ne suka nuna sha`awar takarar shugabancin jam`iyyar, amma jiga-jiganta sun yanke shawarar bin hanyar maslaha yayin zaben.

Bakwai daga cikinsu, Mallam Saliu Mustapha da da Mallam Mohammed Etsu da da Sanata Mohammed Sani Musa da Sanata Tanko Al-Makura da Sanata George Akume da Senata Abdullahi Adamu duka daga shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya ne.

Sai na takwas, wato tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar arewa maso yamma. Sannan akwai Sanata Ali Modu Sharif, wanda `yan kwanaki gabannin taron ya ce ya janye saboda ya hangi cewa akwai wani shiri da ake yi don daidaitawa a bar kujerar ga wani dan takara, kuma a cewarsa Shugaba Buhari na goyon bayan shirin maslaha ko daidaitawar.

Kuma a karshe maganar ta tabbata, saboda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, kuma jami`i a kwamitin yaɗa labarai na babban taron ya ce maslaha za a bai wa fifiko, kuma abin da jiga-jigan APC suka kashe dare suna yi kenan, suna ban-baki ga sauran ƴan takara domin su mara wa mutum guda.

Har ma an ba da umurnin jam`iyya ta mayar musu da kudin da suka kashe wajen yankan fam:

Tun tuni dai rahotanni ke cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ne shugban kasa da jiga-jigan APCn suka sanya wa albarka don zama shugaban jam`iyyar kuma har yanzu fadar shugaban kasa ba ta musanta ba.

BBC ta tuntuɓe shi don jin ko da wani ɗar-ɗar da zuciyarsa ke yi idan aka ce zabe za a yi maimakon maslaha. Sai ya ce maslaha alheri ce amma idan ta kama a yi zabe ko gezau!

Abin da zai biyo bayan taron, shi ne babban kalubalen da masana siyasa ke jinjinawa saboda sarkakiyar da ke ciki ganin cewa shugaban rikon jam`iyyar, wato gwamnan jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni da ake yi wa lakabi da limamin sulhu zai tafi.

Wasu masanan dai na cewa watakila wasu da ba su samu yadda suke so ba ka iya ficewa daga jam`iyyar. Wasu kuma za su tsaya da nufin yi mata zagon-ƙasa ko ƙafar-angulu a babban zabe.

Amma komai ya dogara ne ga salon da jam`iyyar ta yi amfani da shi wajen lalama da ɗinke baraka a tsakanin `ya`yan nata.