Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ga watan azumin Ramadan na 2022 a Najeriya
Kwamitin duban wata a Najeriya ya sanar da cewa an ga watan azumin Ramadan na shekarar 2022 a wasu sassan ƙasar.
Hakan na nufin a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun 2022 za a tashi da azumin a matsayin 1 ga watan Ramadan na shekarar 1443 bayan Hijira.
Sanarwar ta Najeriya ta zo ne bayan da ƙasar Saudiyya ta sanar da nata ganin watan tun da yammacin 1 ga watan Afrilun, wato sa'o'i kadan kafin ganin na Najeriya.
Kwamitin ganin watan wanda ya wallafahakan a shafina na Tuwita ya ce an gan shi ne a garuruwan Bauchi da Gombe da Azare da Misau da Numan da Legas da Kaduna da Abuja da Bajoga da Nafada da kuma birnin Maiduguri da wasu da dama.
A can Jamhuriyar Nijar ma rahotanni sun ce an sanar da ganin watan azumin.