Kalubale biyu da ke gaban sabon shugaban jam'iyyar APC

Abdullahi Adamu

Asalin hoton, APC

An wallafa

Duk da cewa jam'yyar APC mai mulki a Najeriya ta yi nasarar gudanar da babban taronta lami lafiya a ranar Asabar inda aka sanar da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugabanta masana sun ce akwai manyan kalubale dake gaban sabon shugaban jam'iyyar da kuma mukarabansa.

Dr Abubakar Kari wanda malami ne a sashin kimiyar siyasar da ke jami'ar Abuja ya ce kalubalen nada yawa amma muhimai daga ciki sun hada da:.

Rashin hadin kai tsakanin 'yayan jam'iyyar

A cewar masanin akwai rarabuwar kai sosai a cikin jam'iyyar ta APC musaman idan aka dubi da cewa jam'iyya hadaka ce da ta kunshi bangarori daban daban kuma kawo yanzu ta kasa dunkewa wuri guda bayan shekara takwas da kafuwarta

"Kusan shekara 8 zuwa 9 kennan da kafa jam'iyyar amma har yanzu wadanan kungiyoyi sun kasa dunkulewa wuri guda su zama jam'iyya , har yanzu kowa kukan gidansu yake yi to wannan babban kalubale ne" in ji shi .

Ya zaa dole ga Abuduklahi adamu da mukarabansa dole n esu yi hobbasa ganin cewa jamiyyar APC ta zama jamiyya amma ba kungiya mai bangaririun daban aban ba

Zaben fid da gwani

Masanin ya kuma bayyana zaben fid da da gwani a matsatin wani babban kalubalen da ke gaban Sanata Abdullahi Adamu.

A cewarsa wannan shi ne kalubalen da sabon shugaban jam'iyyar zai fara fuskanta a cikin watani biyu masu zuwa saboda zabe ne da za a yi a matakai daban daban domin tunkarar zaben 2023.

" Wannan babban kalubale na kwarai da gaske musaman ganin cewa akwai hamshakan 'yan siyasa. Masu buri wanda kuma kowanensu ya watsa wukarsa kuma zasu dage akan cewa sai sun yi nasara," in ji shi.

Dr Kari ya ce zama dole ga Sanata Abdullahi Adamu da mukarabansa su yi hobbasa ganin cewa jam'iyyar APC ta zama jam'iyya amma ba kungiya mai bangarori daban-daban ba.

Sai dai gabanin zaben jam'iyyar ta tsinci kanta cikin wani mumunan na hayaniya da rikice-rikice a tsakanin manyan shugabaninta da kuma kokwanton da aka rika yi a kan ko za ta iya gudanar da babban taronta da kuma shakkun da ake yi game da makomarta a matsayin jam'iyya mai mulki shi ya sa wasu masana su ke ganin wannan babbar nasara ce ga jam'iyyar.

Sun kuma nuna damuwa a kan tsarin da aka bi wajen amincewa da Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar. Sun nuna damuwa akan yadda tsarin uban gida ke ci gaba da tasiri a harkar siyasar kasar kamar yadda Dr Abubakar Kari ya bayanna.

" Babban abin la'akari kuma mai tasiri shi ne hanyar da aka bi aka zabesu saboda hanya ce wadda aka saba gani , hanya ce wadda idan kana son shugabanci,to dole sai ka yi kamun kafa ta wurin wani uban gida saboda haka gaba dayan su wadannan shugabannin kwamitinin gudanarwa na jamiyyar APC zaa iya cewa shafaffu da mai ne wadanda iyayen gidajensu ne suka daukesu suka dora su a kan wannan mukami kuma wadannan iyayen gidan sun hada da shugaban kasa da kuma gwamnoni''.

A cewar masanin : ''Ba zabe aka yi ba, an ce anyi masalaha ne kuma masalahar irin ta tilastawa.

Wadanda duk suka nuna aniyyar takara da dama daga cikinsu an tilasta mu su, dole su ka yi hakuri suka bada wuri ga su wadannan shafafu da mai''

Masanin ya ce irin wannan abu ya fara zama al'ada a harkar siyasar kasar ta wannan jamhuriya sai dai ya yi gargadin cewa wannan ba al'ada ba ce mai kyau saboda ita siyasa abinda ta gada shi ne ayi takara a fito a fafata a yi zabe amma ba ''dauki dora'' kamar yadda mu ka gani ba.