Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
MDD ta bukaci a kare fararen hula tare da sukar Rasha a kan Ukraine
Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da a tabbatar da kare farar hula a yakin da ake yi a Ukraine, sannan kuma ya soki Rasha da laifin haddasa mummunan yanayi na tsananin wahala ga jama'a.
Matakin wanda Ukraine ta gabatar ya samu gagarumin goyon baya, inda kasashe biyar kawai suka ki amincewa da shi, kasashen su ne, ita kanta Rasha da Syria da Koriya ta Arewa da Eritrea da kuma Belarus.
Da take kalubalantar matakin, Rasha ta ce, ya karkata bangare daya ne kawai, wato na sukarta, wanda a kan hakan ita kuma ta nuna goyon bayanta ga wani kudurin na daban kishiyar wannan, wanda shi kuma Afirka ta Kudu ce ta gabatar da shi ga babban taron na Majalisar Dinkin Duniya.
A kudurin, Afirka ta Kudu ta yi kira ga dukkanin bangarorin da ke yakin ba tare da ta ware Rasha ita kadai ba, ta yi kira da su dakatar da hare-hare, tare da mayar da wuka kube.
Sai dai kuma babban taron na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar kin amincewa da kudurin na Afrika Ta Kudu bayan da Ukraine ta yi zargin cewa Rasha ce a fakaice ta kitsa shi.
Jakadiyar Amurka a Majalisar ta Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, ta gaya wa manema labarai cewa duniya ta hada kai ta kuma tsaya tare a adawa da mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine.
Ta ce, ''A yau ma duniya ta sake hada kai. Ta tsaye tare saboda mamaya ta rashin gaskiya da Shugaba Putin ya yi wa Ukraine haka kawai. A tare, kakkarfar gamayyar kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya ta nuna karara cewa Rasha ce ke da alhakin matsananciyar matsalar da jama'a suka shiga da kuma tashin hankali a Ukraine.''
Ta kara da cewa "Vladimir Putin ba zai ga nasara ba a Ukraine, kuma a yau mun ji cewa ba zai ganta ba ma a New York."
Haka su ma a taron dangin da suka yi kan batun mamayen Ukraine din da Rasha ke yi, kungiyar tsaro ta NATO da Tarayyar Turai da kuma kasashe masu karfin masana'antu G7 a Brussel, sun nuna gagarumin hadin kai da goyon baya a tsakanin shugabannin kasashen Yamma.
Shugaba Joe Biden na Amurka da Ursula von der Leyen, ta Hukumar Tarayyar Turai sun ce kansu ya hadu wurin mayar wa Rasha martani kan yakin rashin gaskiya da adalci na haka siddan da ta kaddamar a Ukraine.
Mista Biden ya bayyana Shugaba Vladimir Putin, a matsayin mamugunci, wanda ke samun sabani ko kishiyar abin da ya yi niyyar samu lokacin da ya kaddamar da mamayar, wata daya da ya wuce.
Da yake magana da BBC, Shugaban Latvia Egils Levits, ya yi gargadin cewa mamayar ta gwamnatin Rasha ba Ukraine kawai take nufi da ita ba, abin ya fice haka.
Ya ce, ''Rasha na barazana ga NATO, barazana ga Turai, barazana ga dukkanin kasashe masu dImokuradiyya a duniya. Aniyar Rasha ita ce ta sake dawowa tare da fadada daular Rasha, kuma a wannan aniya ba ta da wata iyaka. Rasha za ta dakata ne kawai idan ta gamu da gagarumin karfin da ya yi mata turjiya a niyyarta, kuma wannan gagarabadau, ita ce kungiyar NATO.''