Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwamitin Sulhu na MDD zai gana saboda zargin Rasha kan Ukraine
Jami'an diflomasiyya a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun ce za su yi wata ganawa a ranar Juma'a, saboda bukatar da Rasha ta gabatar ta tattauna zargin da ta yi cewa Ukraine na yin makamai masu yaɗa kwayoyin cuta da taimakon Amurka.
Washington ta yi watsi da zargin na Moscow, wanda daman zargi ne da fadar gwamnatin Rashar ta yi ba tare da ta gabatar da wata shaida ba, kamar yadda rahotanni suka nuna.
Zargin na Rasha tun da farko ya gamu da suka daga Amurka da cewa ba kamar yadda Moscow ta yi ikirarin cewa Washington na taimaka wa Ukraine wajen yin makamai masu guba ko kuma masu lalata laka.
Ita kanta Rashar za ta iya fakewa ta yi amfani da makaman domin ta dora alhakin hakan a kan abokan gabarta na Ukraine.
Mataimakin jakadan Rasha a Majalisar ta Dinkin Duniya, Dmitry Polyansky, shi ne ya sanar da gayyatar da 'yan kwamitin tsaron na Majalisar ta Dinkin Duniya kan tattauna maganar, kamar yadda ya nuna a wani sakonsa na Twitter.
Shugaba Volodymyr Zelensky, na Ukraine ya yi magana kan wannan zargi na Rasha a jawabinsa da ya yi wa 'yan kasarsa a baya-bayan nan:
Ya ce, ''sun zarge mu, mu suka sake! Cewa wai muna hada makamai masu yaɗa cutuka.
Wai muna shirin kai hari da makamai masu guba. Wannan abu ya dame ni, saboda mun gamsu sosai cewa , idan kana son fahimtar shirin Rasha, to kawai ka dubi abin da Rasha ke zargin wasu da aikatawa.
Duba da yadda irin wadannan zarge-zargen kafar watsa labaran Rasha, hakan na nuna su ne za su iya yin hakan. Sojojin Rasha da hukumar leken asiri ta Rasha kenan.
Daman tuni sun taba yin hakan a wasu kasashen. Su ne za su yi zargin, su ne za su tsara. Kuma haka za su yi ta yi, idan ba a taka musu burki ba.'' in ji shugaban.
Da yake bayani ga kwamitin bayanan sirri na Majalisar dattawan Amurka, darektan hukumar leken asiri ta kasar, CIA, William Burns ya bayyana zargin na Rasha a matsayin wata dabara.
Tun da farko kakakin ma'aikatar tsaro ta Rasha Igor Konashenkov ya yi ikirarin cewa Amurka na taimaka wa Ukraine kirkiro makamai masu guba, da wadanda ke yada kwayoyin cuta.
Sannan tare kuma da yin amfani da tsuntsaye masu daukar kwayoyin cuta na 'yan mitsi-mitsin halittu na bairus, tsuntsayen da ke bi ta Rasha.
Yayin da ake ta daukar matakan karya lagon Rashar ta hanyar sanya mata takunkumi saboda mamayen na Ukraine, Shugaba Vladamir Putin ya lashi takobin mayar da martani:
Ya ce, '' Daman tun tuni muna cikin matsin takunkumi, to amma ba shakka na yau daban yake, kuma yana taso da wasu tambayoyi, matsaloli da kalubale gare mu.
"To amma za mu ga bayansu kamar yadda muka ga bayan na shekarun baya. Dole ne mu wuce wannan lokaci, ba shakka tattalin arzikin zai jure ya kuma saba da sabon yanayin."
A halin da ake ciki kuma rahotanni na cewa wani tsohon sojan Kanada, wanda gwani-na-gwanaye ne a duk duniya wurin iya labewa a yi harbi daga nesa, ya sauka Ukraine domin taimaka wa sojojinta a yakin da suke yi da Rasha.
Kwararren mai shekara 40, wanda ba a bayyana sunansa ba, illa inkiyarsa ta soji.
Wali ya yi yaki a Afghanistan inda aka ce ya rika hallaka abokan gaba da dama daga nisan mil biyu wato kilomita 3.2.
Haka kuma an ce ya yi yaki tare da dakarun kurdawa a fafatawarsu da mayakan IS a Iraqi.
Gidan rediyon gwamnatin Kanada ya ce, mutumin ya je Ukraine din tare da wasu tsoffin sojojin Kanadar uku, inda ya gaya wa rediyon cewa, ''ina son in taimake su ne kawai.''
''Ana yi wa mutane ruwan bama-bamai kawai don suna son su zama 'yan Turai ba Rashawa ba.''
Hukumomi sun ce kusan mutum 20,000 ne suka kai kansu, daga gomman kasashe, domin aikin sa-kai na taimaka wa Ukraine a yakin da Rasha.