MDD ta yi roko da a bar farar hula su fice daga Ukraine

An wallafa

Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya yi roko ga dukkanin bangarorin da ke yaki a Ukraine da su tsahirta bude wuta, su kuma bayar da dama ga fararen hula su fice daga kasar.

Martin Griffiths, wanda ya yi rokon a yayin taron gaggawa da kwamitin tsaro na majalisar, ya bayyana yadda rayuwar miliyoyin mutane wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba ta balbalce.

Babban jami'in ayyukan jin-kan na Majalisar Dinkin Duniyar, ya yi wannan roko ne cikin yanayi na tausayawa da alhini na irin halin da ya ce miliyoyin mutane farar hula suka samu kansu a tsakiyar wannan rikici da ke shiga rana ta 12 da mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine, abin da ya haifar da tashin hankali da tsoro da ciwo.

Mista Griffiths ya yi roko da a bar fararen hula su fice salin-alin daga yankunan da Rasha ke kai farmaki, kuma a bar jama'a su nufi inda duk suke so, ba tare da an tilasta ko cewa za a zaba musu inda za su nufa ba.

Haka kuma jami'in ya roki da a bayar da dama ga Majalisar Dinkin Duniya ta kai kayan agaji musamman na kula da lafiya da ake matukar bukata, ga birane irin su Mariupol da Kharkiv.

Mista Griffiths ya ce akwai bukatar a samu hanyar sadarwa ta koda yaushe kuma ya ce ya aika da jami'ai Moscow domin samun damar yadda za a tsara aikin agaji yadda ya kamata.

A yayin taron na gaggawa na kwamitin tsaron, jakadiyar Amurka a majalisar, Linda Thomas-Greenfield, ta ce hotunan munanan abubuwan da ke faruwa a Ukraine na tayar da hankalin duniya:

Ta ce, ''Wadannan hotuna na gidaje da asibitoci da makarantu da gidajen marayu da ake lalatawa da bannatawa a gaban idonmu na tayar da hankalin duniya.

"Yara masu cutar daji ba sa samun damar a yi musu magani, ana haihuwar jarirai a dakunan karkashin kasa, maimakon wuraren haihuwa na asibiti, kuma daruruwn dubban fararen hula ba su da lantarkin dumama wurarensu ko ruwan sha da za su rayu.''

Shi kuwa Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya musanta cewa gwamnatin kasarsa ce ke hana fara hula ficewa domin tsira:

Ya ce, ''Wakiliyar dindindin ta Amurka a yau ta zarge mu da kin cika alkawarinmu na samar da damar ficewar jama'a. Bari mu warware wannan.

''Muna kara jaddada cewa hadarin da fararen hula ke ciki a Ukraine ba sojojin Rasha ba ne, saboda ba ruwan bama-bamai muke musu ba, 'yan Ukraine ne masu tsattsauran ra'ayi da akidar 'yan Nazi, su ke garkuwa da garuruwa da birane gaba daya, su yi garkuwa da jama'a, su hana jama'a fita, duk da cewa akwai damar yin hakan. Kuma ga shi sojojin Rasha sun dakatar da bude wuta. Akwai tarin misalan wannan.'' in ji jakadan na Rasha.

Wannan dai na kasancewa ne yayin da Ukraine ke zargin Rasha da ci gaba da ruwan bama-bamai, abin da ta ce ya hana kwashe ko ficewar fararen hula daga garuruwa da biranen da Rashar ta yi wa kawanya, kamar su Kyiv da Mariupol da Sumy da kuma Kharkiv.

Haka kuma Ukraine ta ki amincewa da maganar barin fararen hula su fice bayan da ta lura cewa yawancin hanyoyin da fararen hular za su bi, za su shiga Rasha ne ko kuma kawarta Belarus.

Zagaye na uku na tattaunawar samar da mafita ga fararen hular ya kawo karshe, inda wani jami'in Ukraine ke cewa ci-gaban da aka samu ba wani babba ba ne.