Tsohuwar Sakatariyar harakokin wajen Amurka Madeleine Albright ta mutu

Asalin hoton, Getty Images
Madeleine Albright, mace ta farko da ta zama sakatariyar harkokin wajen Amurka, ta rasu tana da shekaru 84.
Albright ta zama babbar jami'ar diflomasiyya a 1997 zamanin mulkin Clinton, inda ta zama macen da ta taɓa riƙe babban muƙami a gwamnatin Amurka.
Ana jinjina mata a matsayin "jarumar dimokuradiyya," Albright ta taka rawa wajen kawar da ƙabilanci a Kosovo.
Ta mutu ne sakamakon ciwon kansa, kamar yadda ma'aikatar harakokin waje ta bayyana.
"Kullum tasirin da ta yi a wannn ginin ba zai taɓa gushewa ba," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harakokin wajen Amurka.
An haife ta a Prague a 1937 a tsohuwar ƙasar Czechoslovakia - asalin sunanta Marie Jana Korbelova kafin ta sauya zuwa Madeleine Albright - Albright ɗan jami'in diplomasiyar Czechoslovakia wanda aka tilastawa yin ƙaura bayan ƴan Nazi sun mamaye ƙasarsa a 1939.
Ta koma Amurka a 1948, shekarar da iyalinta suka nemi mafakar siyasa.
Ta zama ƴar Amurka a 1957.









