Waiwaye: An kashe DPO a Neja, 'haƙurin da Buhari ya bayar bai isa ba'
Daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon akwai umarnin kotu na goge wani sashe a Dokar Zaɓe ta 2022 da kuma ci gaban da aka samu a rikicin jam'iyyar APC mai mulki.
Kamar kowane mako, mun duba muhimman abubuwan da suka faru.
Wasu 'yan Najeriya na cewa haƙurin da Buhari ya bayar bai isa ba

Asalin hoton, State House
Bayan shafe fiye da wata 'yan Najeriya na fama da matsalar ƙarancin man fetur, wasu 'yan ƙasar na cewa haƙuri da neman afuwar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi bai isa ba.
Mafi yawan ma'abota shafukan BBC Hausa da suka bayyana ra'ayoyinsu ba su gamsu da kalaman shugaban ba, suna masu cewa "kayan masarufi ma sun yi tsada".
Buhari ya bai wa mutanen kasar hakuri kan matsalar rashin wuta da wahalar fetur da ake fama da su cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
"Gwamnatinmu na aiki ba dare ba rana domin ganin an kawo karshen wannan matsala. Kuma shirin da aka tsara a farkon wannan wata za a aiwatar da shi domin tabbatar da an kawo karshen karancin man da ake fama da shi," in ji shi.
Wani mai suna Abbas Mustapha: "Mu ci hakuri mu mutu. Mun saba jin irin wannan daga gare shi. Ina da tabbacin 'yan Najeriya sun fi kowa hakuri a duniya."
Kotu ta umarci Abubakar Malami ya cire sashe na 84 daga sabuwar dokar zabe

Babbar kotun Najeriya da ke zamanta a Umuahia ta bai wa babban lauyan gwamnati kuma antoni janar na kasar umarnin goge sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka sauya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Mai shari'a Evelyn Anyadike ne ta bayyana hakan a ranar Juma'a inda ta ce wannan sashe baya cikin kundin tsarin mulkin, bai da ce da kundin tsarin mulkin ba, kuma ya saba wa doka, ba shi kuma da ta siri kan komai, kuma saba doka ta ko wacce fuska.
Sashen ya ce: "babu wani wanda aka nada a ko wanne mataki da zai zabi wakili ko za a zabe shi a wani taro na ko wacce irin jam'iyyar siyasa a da zimmar tsayawa takarar a ko wanne irin zabe,"
Alkaliyar ta yi bayanin cewa kundin tsarin mulkin na 1999, karkashin sahe na 66(1)(f), 107(1)(f), 137(1)(f) da 182(1)(f) ya riga ya yi bayani a fayyace kan cewa duk wanda ke da mukami a gwamnati da ke neman takara sai ya ajiye mukaminsa da kwana 30 kafin ranar zabe, amma ko wacce irin doka ce ta nemi wadannan masu mukamai su ajiye mukamansu ko kuma su bar ofis a kowanne lokaci kafin wannan lokaci to ta sabawa doka.
Kotu ta amince APC ta gudanar da babban taronta

Asalin hoton, Mai Mala Media
Wata babbar kotu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin kyale jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekarar.
A ranar Juma'a alkalin kotun, Mai shari'a Bello kawu ya yanke hukunci cewa 'ya'yan jam'iyyar ba su da hurumin kai kararta.
Ya ce wani umarnin Kotun Kolin Najeriya kan wani batu irin wannan ya sha gaban wanda babbar kotun ta fitar na 18 ga watan Nuwambar bara.
Kotun ta daga zamanta zuwa ranar 30 ga wannan watan na Maris domin ci gaba da sauraren karar.
Wani mamba a jam'iyyar mai suna Salisu Umoru ne ya shigar da kara inda yake so kotun ta hana jam'iyyar ta APC da gwamna Mai Mala Buni da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC su shirya babban taro na kasa na jam'iyyar har sai bayan an kammala sauraren karar da ya shigar.
A gefe guda kuma, Mai Mala Buni, gwamnan Jihar Yobe kuma shugaban kwamatin riƙo na shugabancin APC ya koma ƙasar daga tafiyar neman lafiya tare da ci gaba da aikinsa a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Gwamnan ya koma a ranar Alhamis kwana ɗaya bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Landan.
Buhari ya bukaci kungiyar gwamnonin APC ta bar Mai Mala ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar bayan wasu gwamnonin sun so a sauya shi da Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello.
Buhari ya ce ya fahimci rigimar da ke faruwa a cikin jam'iyyar lamarin da ya sa aka kai kara kotu, yana mai cewa duk da haka ya amince Mai Mala Buni ya ci gaba da jagorancin babban taron jam'iyyar da ake shirin gudanarwa a ranar 26 ga watan Maris, duk da wani umarnin kotu da ya ce a dakatar da taron.
Kazalika a wata wasika da shugaban kasar ya aike wa shugaban gwamnonin jam'iyyar APC, Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, Shugaba Buhari ya bukaci a guje wa abubuwan da za su dagula jam'iyyar yana mai cewa "da farko batun shugabancin riko na jam'iyya zai komo kamar yadda yake a baya."
Hakan na faruwa ne a yayin da Jam'iyyar APC ta jaddada cewa Mai Mala Buni zai karɓi aikinsa da zarar ya koma gida daga tafiyar da ya yi.
An kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a hanyar Abuja Kaduna

Asalin hoton, AFP
Yan sanda a Najeriya sun ce sun kama wani da ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane ne tare da wasu mutum 29 na daban,
'Yan sandan sun ce mutane suna da hannu a yawancin garkuwar da ake yi da mutane da fashi da makami wadanda suka fi mayar da hankali a kan hanyar Abuja-Kaduna har da ma cikin Kaduna.
Mutumin mai shekara 36 ya amsa cewa shi yake jagorantar kungiyar, cikin wata sanarwa da 'yan sanda suka fitar a yammacin Alhamis.
Hanyar Abuja-Kaduna na daya daga cikin hanyoyi masu matukar hadari a Najeriya yayin da masu garkuwa da mutane ke yi wa matafiya kwantan bauna a hanyar.
Sau da yawa ke kama harbin kan mai uwa da wabi domin tursasa musu tsayawa a hanya.
An kashe matafiya da yawa a hatsaniya wadanda kuma suka tsira sai a yi garkuwa da su kuma ana sakinsu ne bayan sun biya kudaden fansa.
Wannan dalili ya tilastawa mutane da dama daina bin hanyar suka koma jirgin kasa - wanda suke ganin hakan a matsayin wani tudun mun tsira daga bin hanyar.
Ƴan bindiga sun kashe DPO a Jihar Neja

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun ce 'ƴan bindiga sun yi wa ofishin ƴan sanda a Nasko ƙofar rago tare da kashe jami'in an sanda mai muamin DPO.
An kashe DPO Umar Mohammed Digari ranar Talata da wasu 'ƴan sanda biyu, kamar yadda jaridar PRNigeria ta ruwaito.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar cewa ƴan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne bayan harin da aka kai masu a maɓuyarsu inda aka ƙwace shanun da suka sato sama da 800.
Sai dai babu wata sanarwa daga rundunar ƴan sandan jihar da ta tabbatar da lamarin.
'Yan sandan Najeriya sun kama mutanen da ake zargi da yi wa mace tsirara a titi

Asalin hoton, Other
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum shida da zargin yi wa wata mata tsirara tare da yin holenta a titi.
Lamarin ya faru ne a garin Aguleri da ke Jihar Anambra a kudancin ƙasar bayan mutanen sun zarge ta da hannu a mutuwar mijinta saboda lalata da take yi da wasu mazan, zargin da ta musanta.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani mai maganin gargajiya da ya kula da mijin nata, wanda daga baya ya faɗa wa 'yan uwansa cewa matar na da hannu wajen mutuwarsa.
'Yan sanda sun kama mutanen bayan wani bidiyo ya karaɗe shafukan zumunta, inda ya nuna mutanen suna yawo da matar a titi tsirara. 'Yan Najeriya da dama sun nuna ɓacin ransu da ganin bidiyon.
Mai magana da yawun 'yan sandan Anambra ya faɗa wa BBC cewa suna gudanar da bincike kan mutanen da suka kama da zargin abin da suka kira laifin cin zarafi kafin a kai su kotu.
'Najeriya za ta fuskanci giɓin kuɗaɗe a fannin haƙo ɗanyen mai'

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwararru sun fara tsokaci a kan asarar da Najeriya za ta iya yi, saboda kamfanin haƙo man fetur na Eni ya ayyana cewa ba zai iya cika alƙawarin man da ya ke fitarwa zuwa ƙetare ba.
Lamarin ya faru ne sakamakon fasa bututun mai a tashar haƙar man fetur ta Brass a yankin Nembe cikin jihar Bayelsa.
Kamfanin ya ce al'amarin zai haddasa giɓin sama da gangan dubu ashirin da ya ke samarwa a kullum.
Eni ya ce ba zai iya cimma yarjejeniyar samarwa wadanda za su sayi mai daga gare shi ba, sakamakon fashewar da bututan da ke daukar mai daga rijiyoyi zuwa wasu tashoshi a jihar Bayelsa.
Bugu-da-kari kamfanin na Eni ya ce ko a karshen watan jiya ma, sai da bututan mai a tashar Obama suka fashe al'amarin da ya janyo katsewar ganga dubu biyar daga man da ake hakowa.
Ko me hakan yake nufi Eni ya ce ba zai iya cika alkawarin fitar da mai ba?, Dr. Ahmad Adamu masanin tattalin arzikin man fetur a Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewa daman man fetur din da kamfanin Eni ke fitar bai taka kara ya karya ba.











