Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chris Hugton na daf da zama sabon kocin ƙungiyar Black Stars ta Ghana
Ana daf da sanar da Chris Hugton a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ghana wato Black Stars bayan sallamar kocin ƙungiyar ɗan ƙasar Serbia, Milovan Rajevac.
Tsohon kocin na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brighton & Hove Albion ya shafe kusan mako guda a ƙasar Ghana inda a halin yanzu rahotanni ke cewa ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ghana domin ya zama sabon kocinta kamar yadda jaridun ƙasar suka ruwaito.
Majiyoyi masu ƙarfi a ƙasar sun tabbatar da cewa Mista Hughton ne ma zai jagoranci ƙungiyar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da ƙasar ta Ghana za ta kara da Najeriya a watan Maris.
Bayan isar Mista Hugton Ghana, jama'a da dama na ta ce-ce-ku-ce kan batun gwamnatin ƙasar za ta ba shi jagorancin ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar inda wasu bayanai ke cewa ita kuma ƙungiyar tsohon ɗan ƙwallon ƙasar take so Otto Addo.
Duk da cewa shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ghana Kurt Okraku ya je Borussia Dortmund domin tattaunawa da mataimakin kocinsu wato Otto Addo domin ya zama sabon kocinsu, ana kyautata zaton haƙarsa ba za ta cimma ruwa ba da zaran an sanar da Hughton.
Sai dai idan Ghana ta doke Najeriya ne kawai za ta samu damar zuwa gasar cin kofin duniya wadda za a yi a Qatar a Disamabar bana.