Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Yadda ƴan Najeriya ke zolayar ƴan Ghana bayan fitar da su daga gasar
Jama'a da dama musamman ƴan Najeriya suna ci gaba da zolayar ƴan ƙasar Ghana bayan ƙasar Comoros ta fitar da su daga gasar cin kofin Afrika ta Afcon.
A karawar da suka yi ranar Talata, Comoros ta doke Ghana 3-2 a wasa na uku a rukuni na uku.
Hakan ya jawo aka yi ta ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta inda har batun wasan na Ghana ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake tattaunawa.
Comoros, wadda wannan ne karon farko da take fafatawa a Afcon, ta fara cin kwallo ta hannun El Fardou Ben Nabouhane daga nan kuma aka kori kyaftin din Ghana, Andre Ayew wanda aka bai wa jan kati.
Ahmed Mogni ya kara cin na biyu kafin daga baya Ghana ta farke kwallayen biyu, wasa ya koma 2-2.
Daga karshe Mogni ya kara na biyu a wasan kuma na uku a karawar a minti na 85 da hakan ya sa Ghana ta yi waje a karawar rukuni a karon farko tun bayan 2006.
Me jama'a ke cewa kan wannan wasa?
Jama'a da dama na ta muhawara dangane da wannan wasa na Ghana da Comoros.
Wannan mai suna Man of Letters tsokana yake yi dangane da wutar lantarkin da ƴan Ghana suka yi ta ikirarin sun fi Najeriya samu inda ya ce da fatan wutar da Ghana ke samu za ta haskaka wa ƴan wasanta hanya zuwa gida daga Kamaru.
Wannan kuma ta saka hoton wata ɗauke da jakunkuna da ake kira Ghana Must Go da yawa inda take cewa Ghana har ta soma tafiya.
Wannan kuma mai suna Bunmi tana mayar da martani ne ga wani mai suna Shatta Wale inda take cewa ta goda wa Allah da bai ɗora rashin nasarar da Ghana ta yi ba kan Najeriya.
Wannan kuma yana zaulayar ƴan ƙwallon inda yake cewa shahararrun masu ɗaukar gawa suna rawa ɗin na ne za su je su kwashi yan wasan na Ghana.
Ba wannan ne karon farko ba
Ba wannan bane karon farko da ƴan Najeriya ke zaulayar ƴan Ghana ba a shafukan sada zumunta inda aka yi ta cacar baka.
Ɗaya daga cikin cacar bakar da aka taɓa yi tsakanin ƴan ƙasashen akwai batun dafa-dukar shinkafa inda yan Najeriya ke cewa tasu ta fi ta Ghana daɗi ƴan Ghana kuma ke cewa tasu ta fi ta Najeriya daɗi.
Haka kuma an ta caccar baki a kwanakin baya tsakanin ƴan ƙasashen kan batun wutar lantarki inda ƴan Ghana ke cewa su ba a ɗauke musu wuta inda suka rinƙa zaulayar ƴan Najeriya da cewa ana ɗauke musu wuta.
Haka kuma akwai batun caccar bakar da aka yi ta yi bayan da Twitter ya buɗe ofishinsa a Ghana wanda hakan ya jawo suka yi ta zaulayar ƴan Najeriya.