Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rayan: Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto yaron da ya faɗa rijiya a Morocco
Masu aikin ceto na ci gaba da ƙoƙarin ceto wani yaro ɗan shekara biyar wanda ya faɗa cikin wata rijiya a kusa da birnin Chefchaouen na ƙasar Morocco.
Yaron, mai suna Rayan, ya faɗa cikin rijiyar ne a ranar Talata inda rahotanni suka ce ya faɗa ne a lokacin da yake wasa a kusa da rijiyar da ke birnin Tamorot wanda ke da nisan kilomita 100 daga Chefchaouen.
Ana kyautata zaton ya faɗa ne cikin rijiyar mai zurfin mita 32. A yanzu haka ana ci gaba da rarake gefen rijiyar inda aka gina wani ƙaton rami mai zurfi wanda hakan zai bayar da dama ga maginan su kai inda yaron yake.
Bayan an shafe kwanaki uku ana gina ramin, akwai kimanin mita uku da ya rage a cimma inda yaron yake, amma kuma akwai yiwuwar samun zaftarewar ƙasa.
Domin kauce wa afkuwar zaftarewar ƙasar, ana gina wani rami na biyu a kusa da rijiyar domin kai ga inda Rayan yake inda ake sa ran samun nasara, in ji mai magana da yawun gwamnatin Morocco Mustapha Baitas.
Mahaifin Rayan na gyaran rijiyar ne a lokacin da lamarin ya afku inda ya ce da shi da mahaifiyar Rayan sun damu matuƙa bayan afkuwar wannan lamarin.
"A lokacin, na kawar da idona daga gare shi, yaron sai ya faɗa rijiyar, ko bacci ban sake yi ba", kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labarai ta le360 a ranar Laraba.
Tun a daren Talata hukumar kare farar hula ke jagorantar ceto yaron inda ake aikin ba dare ba rana.
"An kusa ceto wannan yaron," kamar yadda Mista Baitas ya shaida a daren Talata. "Zukatanmu na tare da iyalansa, kuma muna addu'a zai koma tare da iyalansa ba da daɗewa ba."
Duk da cewa yaron ya faɗa cikin rijiyar mai zurfi, amma hotuna da bidiyon da aka ɗauka bayan an zura kemara a cikin rijiyar sun nuna yaron na da rai kuma yana cikin hayyacinsa duk da cewa ya ji ciwo a kansa.
Masu aikin ceto sun jefa masa abinci da ruwa da kuma takunkumin da ke ɗauke da iskar oxygen haka kuma jami'an lafiya na wajen da lamarin ya faru domin jiran fitowar yaron.
Haka kuma jirgi mai saukar ungulu ya isa wurin domin ɗaukar yaron ya tafi da shi asibiti da zarar an ciro shi.
Dubban mutane na ta kallon aikin ceton ta bidiyo a shafukan sada zumunta haka kuma akwai ɗumbin mutane da suka je kallo a wajen da lamarin ya faru.
Ɗan wasan Aljeriya Riyad Mahrez ya wallafa saƙo a shafukan sada zumunta inda yake jaje da kuma neman Rayan ya kasance mai juriya.
Kafafen watsa labarai na lardin na sa ido kan yunƙurin da ake yi na ceto Rayan haka kuma gwamman yan sanda da jandarmomi da sauran rukunan jami'an tsaro na wajen aikin ceton.
Mohamed Yassin El Quahabi wanda shugaban wata ƙungiya ne na hawa tsaunuka da shiga koguna na taimakawa wajen aikin ceton kuma ya shaida wa BBC cewa sakamakon ƙanƙantar ƙofar shiga rijiyar, hakan ya sa ana samun cikas a wajen aikin ceton.
Ya kuma ƙara da cewa masu aikin sa kai na yankin sun ta ƙoƙarin shiga ta ƙaramar ƙofar rijiyar amma ƙofar ta yi ƙanƙanta.
Daya daga cikin masu aikin ceton ya bayyana cewa "da mun matsa kusa, ramin na ƙara tsukewa wanda hakan ya zama abu mai wahala mu wuce - kuma hakan ya zama abu mai wahala mu ceto yaron. Hakan ne ya sa muka fito da wata sabuwar hanya ta ceton wadda ita ce haƙa rami."
Hotunan da aka ɗauka na waurin da lamarin ya faru sun nuna bulldoza biyar waɗanda ke ta haƙa rami a kusa da rijiyar domin kai ga zurfin da Rayan yake.
Mista El Quahabi ya shaida wa BBC cewa wannan kaɗai ce hanyar da masu aikin agaji za su kai ga ceto RAYAN.
Sai dai hukumomi sun bayyana cewa duk wani abu da za a yi da zai shafi bangon rijiyar zai iya yin illa ga yaron mai shekara biyar.
Ana ta tattauna maudu'in #SaveRayan a shafukan sada zumunta har da ƙasashe msu makwaftaka kamar Aljeriya duk da cewa ba a shiri a takanin ƙasashen biyu.