Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan ziyarar Buhari a Sokoto
Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ziyara a jihohin Zamfara da Sokoto masu fama da kashe-kashe na 'yan fashin daji ranar Alhamis, wasu 'yan jihar da 'yan ƙasa sun duƙufa wurin ɗabbaƙa 'yancinsu na faɗr albarkacin baki.
Ko da yake dai ba maganar hare-haren ce ta kai shi Sokoto ba, fadar shugaban ta ce zai wuce Zamfara don jajanta wa gwamnati da al'ummar jihar game da kisan gillar da suka fuskanta daga 'yan bindiga.
Wannan ne karo na uku da Buhari ke kai ziyara jihohin ƙasar cikin wata ɗaya don ƙaddamar da ayyukan da gwamnatocinsu suka aiwatar. Ya je Ogun ranar 13, Kaduna ranar 20 da 21.
Shugaban ya fara tsayawa a Sokoto ne domin ƙaddamar da sabon kamfanin siminti na kamfanin Bua, wanda Abdussamad Isiyaka Rabiu ya mallaka, kafin ya ƙarasa Zamfara.
Sai dai daga baya aka sanar da cewa ya soke ziyararsa zuwa jihar Zamfara a ranar Alhamis sakamakon rashin kyawun yanayi da ya jawo hazo.
Daya daga cikin masu taimaka masa a shafukan sada zumunta Buhari Sallau ne ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook.
Bashir Ahmad mai taimaka wa Buhari kan kafafen sada zumunta ya ce kamfanin zai dinga samar da tan miliyan uku na siminti duk shekara.
"Shugaba Buhari zai kai ziyara Gusau (babban birnin Zamfara) a yau don yi wa gwamnati jaje da kuma al'ummar jihar. Ina fatan ziyarar ta kawo mana sauyi mai amfani," a cewar wani ɗan jarida daga yankin mai suna Yusuf Anka.
Me 'yan Najeriya ke cewa game da ziyarar?
Wasu 'yan Najeriya mazauna Jihar Sokoto da BBC ta tattauna da su sun bayyana fatan zuwan na Buhari ya zama alkairi.
Sai dai wasu sun soki shugaban kan ƙin yin ziyarar da wuri; a lokacin da 'yan fashin daji suka dinga kai hare-hare tare da kashe mutane.
"Mu dai 'yan Sokoto ba za mu ce ba mu ji daɗin zuwan shugaban ƙasa ba, amma gaskiya za mu iya cewa hakan da ya yi ba mu ji daɗi ba. Saboda abubuwa sun faru a Sokoto ba zo ba sai yanzu da aka ce za a buɗe wani kamfanin siminti," a cewar wata Basakkwaciya.
Wata kuma ta ce: "A matsayina na 'yar Sokoto, ina farin ciki da ziyarar Shugaba Buhari don buɗe kamfanin na Bua. Ina farin ciki sosai."
Marzuk Lawal Kaura, mabiyin shafin BBC a Facebook wanda ya ce Bazamfare ne ya ce "idan har da gaske jaje zai zo mana ai ƙauyukan da lamarin ke afkuwa ya kamata ya je, ba wai ya tsaya a Gusau ba".
"Muna ƙara tuna wa Sarkin Musulmi ya ci gaba da jaddada wa shugaban kasa irin halin da 'yan Najeriya suke ciki na tsananin rayuwa da kisan gillar da ke faruwa a kullum," a ra'ayin Bilal Abubakar daga Facebook.
Wani mai suna Nura Muhammad Abdullahi a Twitter tambaya ya yi cewa "sai yanzu?'.
Shi kuma wani mai suna Sageer Musa, a Twitter dai, ya yi tambaya cewa: " Me ya sa lokutan baya ba ya zuwa kowace jihar cikin arewa domin yi mu su ta'aziyya sai yanzu domin ya ga kwadayayyun mulki sun je?".
Abin da ake cewa a shafin BBC
A shafin BBC Hausa ma mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kamar haka;
Ahmad Sulaiman Bajoga: "Muna fatan wannan ziyara da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a jihohin Sokoto da Zamfara za ta mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro da wadannan jahohi ke fama da su.
Don a samu hanyoyin magance su.
Salisu Abubakar: Allah ya saka wa Shugaba Buhari da Alkairi Allah ya sa zuwansa ya zamo silar kawo karshen wannan masifar ƴan ta'addan a jihar Sokoto.
Abdulwahab Jazuli: Hhhmmm yaudara kenan. Me yasa kwanakin baya duk hatsaniya da kashe-kashen da ake yi bai je ba. An ƙona mutane a mota bai je ba - amman sai yanzu da ka ga siyasa ta matso shi ne ka wani lallaɓo, hhmmm.... Yaudara kawai.
Buhari a Zamfara
Tun a jajiberin ziyarar, gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa'a uku a yayin ziyarar ta shugaban ƙasar.
Gwamnatin jihar ta ce shugaban na Najeriya zai je Zamfara ne domin jajanta wa al'ummar game da miyagun hare-haren 'yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara, ya shaida wa BBC cewa tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasar.
Ya ce baya ga ta'aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al'ummar ta Zamfara, zai kuma kara wa sojoji da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.
"Ɗaya daga cikin manufar ziyarar shugaban kasar a Zamfara ita ce sanyaya zukatan al'ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su," in ji kwamishinan.
Ibrahim Dosara ya ce: "Ba jajen Anka da Bukkuyum kadai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan wadanda suka rasa wani nasu a hare-haren 'yan bindigar a Zamfara".
A cewarsa, yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da jami'an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu saboda hare-haren.
Tuni dai gwamnatin jihar ta bukaci al'ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban kasar.
Sai dai duk da wadannan shirye-shirye daga ƙarshe sai hazo ya hana shugaban zuwa Gusau.