'Yan Taliban na tattaunawa da kasashen Yamma a Oslo

An wallafa

A karon farko tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace mulki a Afganistan, 'yan kungiyar na tattaunawa da wasu jami'ai na kasashen yammacin Turai a Norway.

Ana sa ran tattaunawar ta kwana uku za ta duba batutuwa kamar kare 'yancin dan Adam da kuma matsalolin rayuwa da miliyoyin 'yan kasar ke fuskanta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 95 cikin 100 na 'yan Afghanistan ba su da isasshen abin da za su ci.

Wasu masu zanga-zanga a kasashen Turai sun soki abin da suka kira kyautatawa Taliban da ake yi ta hanyar wannan tattaunawar.

A ranar Lahadi, wasu mambobin Taliban sun gana da masu fafutukar kare hakkin dan Adam amma ba a bayyana ainihin abubuwan da suka tattauna a kai ba.

Wata mai fafutukar kare hakkokin mata, Jamila Afghani ta shaida wa AFP cewa masu tattaunawar sun nuna da gaske suke yi.

"Za mu ga irin matakan da za su dauka, bisa kalaman da suka furta," inji ta.

Ranar Litinin ita ce ranar da za a yi tattaunawa mafi muhimmanci, inda 'yan Taliban din za su gana da jami'an kasashen yammacin Turai. Kungiyar na son a taimaka ma ta da biliyoyin daloli da Amurka ta kwace a bankunan kasarta.

Kasar Afghanistan na fuskantar karuwar rashin ayyukan yi da hauhawar farashin kayan abinci, yayin da takardar kudin kasar ke kara faduwa sannan bankuna sun hana masu ajiya daukar kudi mai yawa daga asusun ajiyarsu.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi cewa kashi 55 cikin 100 na al'ummar kasar na fuskantar matsalar yunwa.

Shafiullah Azam, wanda wakili ne na Taliban ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa: "Muna yin kira da a sakar wa Afghanistan kaddarorinta kuma a guji azabtar da 'yan kasar saboda dalilai na siyasa."

"Saboda matsalar yunwa, kuma saboda tsananin yanayin sanyi da ake fuskanta, Ina ganin lokaci ya yi da kasashen duniya za su taimaki 'yan Afghanistan a maimakon ladabtar da su saboda rikicin siyasar duniya."