Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Afghanistan ce ƙasar da Kiristoci suka fi fuskantar matsi'
Wata kungiyar agaji da ke tallafa wa Kiristocin da ake tsanantawa ta bayyana Afghanistan a matsayin wuri mafi hadari a duniya ga mabiya addinin.
A cikin rahotonta na shekara, kungiyar, Open Doors, ta ce mamayar da Taliban suka yi a Afganistan na nufin kiristoci na fuskantar gagarumin haɗarin mutuwa idan aka gano imaninsu.
Afganistan ta zarce Koriya ta Arewa a haɗarin zama ga kiristoci inji ƙungiyar.
'Yan Taliban sun tsananta wa ƴan tsirarun addinai dabam-dabam waɗanda ba sa bin tafarkin musulunci.
Sabbin dokoki masu tsanani
A tarihance dai addinin kiristanci na daga cikin addinan da suka jima a Afghanistan, ko da yake ba shi da mabiya da yawa a kasar.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta dai ta soki sabbin dokokin da gwamnatin Taliban ke gabatarwa masu tsanani da ke hana jama'a sukuni, musamman masu alakƙa da mata
Kasashen da ke ba kasar tallafi sun gindaya wa Taliban din sharadin mutunta hakkin mata kafin su dawo da bayar da taimakon kudin da suke yi