Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boris Johnson: Me ya rage wa Firaministan Birtaniya bayan haƙurin da ya bayar kan take doka?
Karɓar laifin da Firaminsitan Birtaniya Boris Johnson ya yi da kuma neman afuwarsa a gaban majalisar dokokin ƙasar ga alama na iya ƙara masa ɗan lokaci.
Wannan wani ɗan jinkiri ne har zuwa lokacin bayyana sakamakon bincike a hukumance kan ko an yi liyafa ko ba a yi ba a fadar gwamnatin, mai yiwuwa cikin mako ɗaya ko fiye da haka.
Amma ga wasu da dama masu goyon bayansa, suna ganin tuni sun dawo daga rakiyar Boris Johnson
To amma Mr Johnson ya buƙaci da a jira sakamakon binciken da ake yi kan batun kafin yanke masa hukunci.
Ƴan majalisa da dama na jam'iyyarsa ma a yanzu so suke ya tafi, inda suke tattaunawa cikin ƙaguwa kan lokacin da za a tsige shi da kuma yadda hakan zai faru.
Wani minista ya shaida wa BBC cewa, "komai ya zo ƙarshe".
Haka ma wani tsohon minista da ya daɗe yana goyon bayan firaministan, cewa ya yi ba su ga wata hanyar tsira da zai samu ba.
Sannan wani tsohon minista ma ya yi hasashen kaɗa ƙuri'ar ko za a amince da ci gaban shugabancinsa a wannan watan.
Ƴan majalisar dokoki na kuma ganin cewa rahoton wata babbar jami'ar gwamnati Sue Gray, ko sake kaɗa ƙuri'a kan sanya dokokin kulle na korona a lokacin da masu ci yanzu suka kawo ƙarshe a ƙarshen wannan watan, ka iya jawo ƙarin buƙatar neman ya yi murabus.
A zahirin gaskiya, babu wani tsayayyen shiri daga ɓangaren abokan hamayyar Boris Johnson.
Akwai jerin sunayen ƴan majalisa masu yawa da wataƙila su nemi kujerar shugabancin, waɗanda yawansu ya wuce mutum biyu da ke gaba-gaban, wato shugaban gwamnati da sakataren harkokin waje.
Haɗin gwiwa
Babu tabbas kan ko za a samu isassun wasiƙu ga jiga-jigan jam'iyyar masu ra'ayin riƙau da za su jawo tsayawa takara daga ɓangarensu a bana.
Babu haɗin gwiwa daga can sama tsakanin ɓangarorin masu ra'ayin riƙau.
Amma masu ra'ayin ƴan mazan jiyan da dama a Majalisar Dokokin sun fi mayar da hankali ne kan lokaci da kuma yanayin tafiyar Boris Johnson, ba wai kan tambayar ko zai iya kai labari ba.
Amma abin kunyar da ya faru na liyafar da aka yi a Fadar Downing Street a lokacin kullen korona ya zama tamkar wakilci ne na ƴan jam'iyyar mazan jiyan: ko Boris Johnson yana da kyawawan halaye da ɗabi'un da zai iya jagorantar ƙasar a Fadar Downing?
Masu ra'ayin mazan jiya da dama na ci gaba da cewa amsar wannan tambaya ita ce 'a'a.
A baya ma Mista Johnson ya sha fuskantar masifu daban-daban, kuma ga dukkan alamu lokacin tafiyarsa ya zo.
Wasu daga cikin abokansa na ganin rahoton Sue Gray ka iya zama wani ƙashin baya na jawabin da zai yi wa al'ummar ƙasar a yau.
Siyasa a wannan zamani ba ta da tabbas. Amma a yanzu an daina tunanin cewa ba zai yiwu Boris Johnson ya rasa kujerarsa ba a nan kusa.