Turkmenistan: Shugaban da ya ba da umarnin rufe ramin wutar da ta daɗe tana ruruwa

The Gateway to Hell crater

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban Turkmen Gurban Bendymukhamedoy ya ba da umarnin kashe wata dadaddiyar wuta da ta jima tana ci a arewacin kasar har ta kai ga zama wani wurin zuwan masu yawon bude ido.

Wurin na nan a bayan babbar hamadar Karakum wadda ta lakume kashi 70 cikin 100 na kasar Turkmenistan, kwatankwacin murabba'in kilomita dubu uku da dari da hamsin.

Wutar ta shafe gwamman shekaru tana ci ita kadai, kuma ba wai don wasu aljanu ko tsafi ko tsubbu ba, sai dai iskar gas din da ke jibge a karkashin kasa.

Shugaba Gurbanguly Berdymukhamedov na son a kalli wannan mataki da ya dauka a matsayin wani yunkuri na bunkasa kasuwancin iskar ta gas har zuwa kasashen duniya.

Yayin wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, shugaban ya ce ''Muna rasa muhimmin arziki daga iskar gas wanda za mu iya amfani da shi wajen inganta rayuwar jama'a''.

Ya umarci mahukunta su nemo hanyar da za abi a kashe wutar.

To sai dai ba wannan ne karon farko da kasar ta yi yunkurin kashe wannan wuta ba, domin hatta a shekarar 2010 ma an yi irin wannan yunkuri.

Yaushe aka yi rijiyar?

The Gateway to Hell crater

Asalin hoton, Getty Images

Mutane da dama sun yi imanin cewa a shekarar 1971 lokacin da masana kimiyyar kasa na tsohuwar tarayyar Soviet na binciken danyen mai ne suka gano iskar gas dankare a wajen, don haka a lokacin da ake kokarin tabbatar da abin da aka gano sai kasa ta rufta a wasu bangarori uku da ke wajen suka zama tamkar rijiya.

A lokacin ne aka rika fargabar fitar iskar, wani abu da ka iya gurbata iska da kuma haifar da masifu iri-iri, a don haka sai aka cinna wa rijiyar wuta bisa tunanin cewa za ta kone gas din kurmus bayan wasu yan kwanaki.

To sai dai wani mai yawon shakatawa na Canada George Corones, ya ce har yanzu bai ga wata hujja da za ta iya tabbatar da wannan labara ba.

A shekarar 2013, wata tawagar kwararru ta isa yankin Turkmen yayin nadar wani shirin talabijin na tashar nan ta haska abubuwan ban mamaki na baiwar ubangiji mai suna National Geographic, sun je wurin ne don gano ainihin lokacin da wannan wuta ta soma ci, to sai dai tambayoyin da suka taso sun haura amsoshin da suka samu.

A cewar masana kimiyyar kasa na Turkeman, an samar da rijiyoyin da wutar ke ci ne a shekarun 1960, daga baya suka kama da wuta shekarun 1980, wato shekaru 20 daga bisani.

''Muhimmin sirri''.

Wani masanin tarihi Geronim Perovic ya ce ba wani abin mamaki bane yadda mutane suke ta camfe-camfe a kan wannan wuta.

Ya fada wa BBC cewa "Wannan wata shaida ce da ke nuna yadda al'amura suka gudana zamanin Tarayyar Soviet, nasarorin da aka samu na siyasa kawai ake sanar da jama'a, amma duk wani shiri da aka fara aka gaza ba a fada wa jama'a, idan ma mahukunta suka yi wani abu to ba za su so jama'a su sani ba.''

The Gateway to Hell crater

Asalin hoton, Getty Images

Wutar na tsakiyar Hamada ne, ba gida gaba ba gida baya, don haka babu fargabar tana iya cutar da jama'a.

Kwararru sun yi imanin cewa a wancan lokaci tarayyar Soviet bata yi fama da karancin gas ba, don haka ba abin mamaki bane idan ta yi almabazzarancinsa ta hanyar kona shi.

Kasa kamar Switzerland na amfani ne da gas din da bai wuce tanka dubu goma sha biyar zuwa sha shida ba a shekara, don haka don Tarayyar Soviet a wancan lokaci ta kona ninki hudunsa ba wani abun a zo a gani bane don ba wani kayan gabas bane a wajenta.

''Kyale ma'adanin iskar gas haka nan ba dabara bace, don haka za a iya fahimtar dalilin daukar matakin kone shi''

''Mun fahimci cewa a wannan lokaci da ake ciki idan har aka ci gaba da kone shi to ba zai iya taruwa wuri guda har a ci gajiyarsa ba, sannan kuma za a iya fuskantar barazanar tashin wuta da kuma fashe-fashe a wurin lokaci zuwa lokaci, gaskiya ne'' inji Jerome Perovic.

Ya ci gaba da cewa har yanzu wannan matsala ce da an kasa sanin yadda za a shawo kanta.

''Muna rasa muhimmin arzikin karkashin kasa da za mu iya amfanuwa da shi, sannan a lokaci guda jama'a za su iya amfanarsa'' in ji shugaban kasar.

A shekarar 2018 ne ya sauya wa wurin suna zuwa "Tauraruwar Karakoom"