Wasiƙa daga Afika: Afrika za ta yi wasanta a 2022 ba tare da babban alƙalinta ba

An yi kewar Desmond Tutu a ranar bikin sabuwar shekara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An yi kewar Desmond Tutu a ranar bikin sabuwar shekara
An wallafa

A jerin wasiƙunmu daga ƴan jaridar Afrika, a wannan karon wani masanin harkokin watsa labarai da ba da horo a harkar Joseph Warungu ya duba mana damarmakin da Afrika ke da su a shekarar 2022.

Short presentational grey line

Shekarar ta fara ne da baƙin ciki sakamakon binne babban mai fafutukar tabbatar da adalci da daidaiton launin fata da kuma 'yantar da siyasa, Archbishop Desmond Tutu a Afirka ta Kudu.

Mutumin da bai taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da rashin adalci ga waɗanda aka zalunta ya mutu ne kwanaki bakwai kacal kafin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 110 da kafuwa.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi fatan gudanar da taron domin sake farfaɗo da farin jinin jam'iyyar a wajen masu kaɗa ƙuri'a domin samun damar sake zabensa a matsayin shugaban jam'iyyar ta ANC.

Za a yanke wannan shawarar ne a babban taron jam'iyyar da za a yi a watan Disamba.

Za a fara gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afrika ranar 9 ga watan Janairu a Kamaru

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Za a fara gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afrika ranar 9 ga watan Janairu a Kamaru

Kwana guda bayan bikin zagayowar ranar kafa jam'iyyar ANC, hankali zai karkata ga kasar Kamaru mai karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 33. Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 24 ne za su fafata a gasar, wadda aka dage sau biyu.

Sudan da Guinea da Mali da kuma Habasha na da manyan dalilan da za su taka rawar gani a gasar don ƙokarin ɗaukar kofin.

Ƙasashe ne da suka fuskanci juyin mulkin soji, ko yunƙurin juyin mulki ko kuma na ƙasar Habasha, yaƙin basasa na tsawon shekara guda wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.

1px transparent line

Ɗaukar gasar cin kofin nahiyar Afirka zuwa gida zai taimaka wajen tayar da hankulan ƙasashen da suka shiga shekarar 2022 da har yanzu suke ta fama da tashe-tashen hankula da rashin tabbas.

Guinea za ta buga wasan cikin fargaba. Sabon shugaban na soji ya gargadi tawagar da ta lashe kofin ko kuma ta mayar da kudaden da aka ba ta.

Tunisiya ta kasance ƙasa mai ƙarfi a filin wasa, amma a cikin gida siyasar ƙasar tana ƙasa tana dabo. Shugaba Kais Saied na fatan zaɓen raba-gardama da za a yi a watan Yuli da kuma zaɓen ƴan majalisar dokoki a ƙarshen wannan shekara zai kwantar da hankula.

Ƴan Tunisiya da dama sun goyi bayan matakin da ya ɗauka na karɓar madafun iko a watan Yulin da ya gabata, tare da fatan hakan zai inganta tattalin arziƙi. A yanzu da dama na ganin shi ne matsalar kuma sun fito zanga-zangarsu kan tituna.

Ba kamar sauran ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Arewacin Afirka - Morocco, Masar da Tunisia ba, Libya ba za ta shiga gasar cin kofin duniya ba.

Ƙasar dai na da babbar matsala wajen shirya zaɓen shugaban ƙasa, wanda ya kamata a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba amma aka ɗage zaben. Ana dai kallon zaben a matsayin wani muhimmin abu na fitar da kasar Libya daga cikin tashe-tashen hankula na tsawon shekaru goma da suka biyo bayan tumɓuke shugaban ƙasar Muammar Gaddafi da kuma kashe shi a shekara ta 2011.

Tsohon Firaministan Kenya Raila Odinga babban mai sha'awar ƙwallon ƙafa ne. Wani lokaci ma yakan yi nasa sharhin wasan kwallon kafa a wajen tarurrukan jama'a don bayyana yadda zai yi da abokan hamayyar siyasa.

A babban zaɓen da za a yi a watan Agusta, ɗan siyasar mai shekaru 76, zai fuskanci wasansa na biyar kuma watakila mafi girma har yanzu bai yi kokarin lashe zaɓen shugabancin kasar ba.

Babban abokin hamayyarsa a yaƙin neman karbar mulki daga hannun shugaba Uhuru Kenyatta, wanda wa'adinsa na biyu kuma na karshe ke karewa, shi ne mataimakin shugaban kasar William Ruto. A halin yanzu dukkan mutanen biyu suna zagayawa kasar suna gudanar da manyan tarukan neman goyon baya.

A Najeriya shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mai da hankali kan lambobi daban-daban domin yana son sanin adadin 'yan Najeriya nawa ne.

A Najeriya shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya mayar da hankali ne kan sanin yawan ƴan ƙasar.

Najeriya ƙasa mafi yawa a Afrika za ta ƙidaya yawanta a bana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya ƙasa mafi yawa a Afrika za ta ƙidaya yawanta a bana

Gwamnatinsa na shirin gudanar da ƙidayar jama'a da ta gidaje a kasar a shekarar 2022. An yi kidayar jama'a ta karshe ne a shekarar 2006 kuma ta ce yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 140. Hukumar kidaya ta kasa ta yi kiyasin cewa yawan mutanen ya karu zuwa kusan miliyan 206 amma jami'ai na son tabbatar da hakan.

Yayin da muke jiran Najeriya ta kirga 'yan Najeriya, duniya za ta yi taro a Masar a watan Nuwamba don mai da hankali kan shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Taron sauyin yanayi na MDD COP27 a birnin Sharm el-Sheikh, zai yi fatan cewa bayan taron Glasgow, kasashe za su yi nazari sosai kan yadda ake fitar da hayaki mai gurbata muhalli, domin taimaka wa duniya wajen takaita dumamar yanayii.

Waƙoƙin Afirka sun ƙara samun tagomashi a lambar yabo ta Grammy. Afirka za ta sami 'yan takara tara idan aka buɗe babban taron a Los Angeles a ranar 31 ga Janairu.

​Wannan ne karo na biyu da aka zaɓi Rocky Dawuni don fafatawa a gasar Grammy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ​Wannan ne karo na biyu da aka zaɓi Rocky Dawuni don fafatawa a gasar Grammy

Wadanda aka zaɓa sun hada da fitaccen mawaƙin nan na Ghana Rocky Dawuni, da tawagar mawakan Afirka ta Kudu Black Coffee, da tsohuwar mawakiyar Benin Angelique Kidjo da Femi da Made Kuti na Najeriya.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ta kasance babbar ƙasa da ta shahara wajen fitar da kiɗa ga sauran ƙasashen duniya baki daya. Kuma a yanzu ƴan Afirka ta Gabas sun sanya ido a kan ƙasar.

Al'ummar kasar dai sun nemi shiga kungiyar kasashen gabashin Afirka (EAC), wadanda suka hada da Kenya, da Uganda, da Rwanda, da Tanzania da Sudan ta Kudu.

Wani bincike da hukumar kasuwanci ta gabashin Afirka ta gudanar ya nuna cewa, kasar Sin ita ce kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa Dimukradiyyar Kongon, wanda ya kai kashi 31.2, sai Afirka ta Kudu mai kashi 15.8 sai Zambia mai kashi 13.

Ci gaban tattalin arziƙin Afirka gaba ɗaya zai ta'allaƙa ne a kan yadda cutar korona za ta ci gaba da yaɗuwa.