Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Australia: Masu zanga-zanga sun cinna wa tsohon ginin majalisa wuta a Canberra
An cinna wa tsohon ginin majalisar kasar Ostreliya da ke babban birnin kasar Canberra wuta na dan wani lokaci jiya Alhamis yayin wata zanga-zanga, inji kungiyar 'yan asalin yankin masu fafutukar neman 'yancin kai.
Babu wanda ya sami rauni a sanadin gobarar wadda ta kama kofofin shiga tsohon ginin kafin aka kashe ta.
Matakin ya biyo bayan makonni biyun da aka shafe ana rikici a birnin a cewar 'yan sandan kasar.
Firaminista Scott Morrisson ya yi tir da tashin hankalin, yana cewa: "Ba haka Ostreliya ta ke ba."
"Wannan abin takaicin ya ba ni haushi wanda ya una yadda 'yan wannan kasar na cinna wa irin wannan alamar demokradiyya wuta."
An dai kwashe dukkan ma'aikatan da ke aiki a cikin ginin.
A yanzu ana amfani da ginin a matsayin gidan tarihi mai suna Museum of Australian Democracy.
A 1988 majalisar kasar Ostreliya ta koma wani sabon gini kusa da wannan a Capitol Hill, daga nana sai aka mayar da tsohon ginin ya zama gidan tarihi.
'Yan sandan yankin babban birnin kasar Ostreliya, ACT sun kaddamar da bincike kan umul-aba'isin gobarar.