Ku San Malamanku tare da Ustaz Aliyu Rasheed Makarfi

An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Wani Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna da ke Najeriya Ustaz Aliyu Rasheed Makarfi ya ce babban abin da ya so shi ne haɗin kan al'umma, musamman da waɗanda ba musulmai ba.

Ya ce mutunta kowa da addininsa da mutuncinsa zai taimaka kwarai da gaske wajen samun ji gaba.

"Na farko a addinance, addinin da nake yi na Musulunci idan zama ya haɗa mu da waɗanda ba Musulmai ba akwai buƙatar zaman lafiya," in ji Sheikh Aliyu.

Ya ƙara da cewa babu abin da yake faranta masa kamar ganin iyali suna zaman lafiya a tsakaninsu, ko ganin abota ta amana.

"Babu abin da ke yi min daɗi illa ganin jama'a sun taso cikin haɗin kai, duk lokacin da na ga wani ya zo ya wuce da iyalinsa ko a kasuwa ko a shago ko masallaci, a rai na na kan yi farin ciki har na kan yi musu addu'a,'' in ji malamin.

Amma kuma akwai abubuwa da malamin ya ce suna ɓata masa rai, kamar ya ga ana cin mutuncin wani, ko ana son tozarta wani.

Tarihin Rayuwa

An haifi Sheikh Aliyu Rashid Makarfi kimanin shekaru arba'in da biyar da suka gabata a garin Makarfi a Karamar Hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna.

Sheikh Aliyu ya taso ne a gaban mahaifinsa, kuma shi ne na 11 a ɗakin mahaifiyarsu.

A hirarsu da BBC, malamin ya kuma bayyana cewa ya fara karatu a makarantar firamare ta garin Makarfi daga nan bayan ya kammala ya tafi kwalejin Barewa ta Zaria, kuma sai Kwalejin Ilimi ta Nuhu Bamalli da ke garin Zaria kafin ya zarce zuwa Jami'ar Bayero ta Kano.

Amma kuma in ji malamin yanzu ya karkata ne wajen al'amuran da suka shafi almajiranci na karantar da addini kasancewar mahaifinsa malam Adamu Rashid shi ne malamin makarantar Islamiyya ta farko a garin Makarfi.

"Wannan ya saka min zumma tun da na taso sai na ga ina da sha'awar abin da mahifinmu ke yi, don haka sa na mayar da hankali wajen karatu tun daga wajen mahaifin nawa," in ji Ustaz Aliyu.

Ya kuma kara da cewa ya kuma yi karatu a wurin malamai da dama da suka haɗa da marigayi Sheikh Usman Ahmed Kauru da marigayi na'ibin Zazzau Alkali Malam Yahuza, da Malam Alu na Zaria.

Sannan ya ce lokacin da yake zaune a Kano ya yi karatu a wurin Malam Mohammed Sani Kaka da marigayi Sheikh Abubakar Imam Ikara da Shiekh Yusuf Sambo Rigachikun.

Ya kuma ya yi karatu a Zaria a gaban Malam Adam Auwal Albani da kuma Farfesa Nuhu Tahir Tajuddeen.

Abinci

Malamin ya bayyana cewa ya fi son tuwon masara wanda yanzu ana sarrafa shi zuwa samanbita da tuwan dawa da na shinkafa, amma idan bai samu ba ya kan ci shinkafa.

"Da yake na yi zaman karkara, ina cin danwake, ina cin gauda, ina cin rummace, ina cin gwarangwaje, ina cin gaigaya, da sauran cimakar karkara," in ji shi.

Ta fannin wasanni kuma malamin ya ce yana yin wasa tare da yaransa, yana buga kwallo a cikin gida, kuma yakan fita gudu yana motsa jiki.

Buri

Malamin ya bayyana cewa yana da burin ganin cewa yana rokon Allah ya azurta shi da kudi na halal da zai gina masallaci da makaranta babba ya kuma danƙa shi zuwa ga al'umma.

"Abu na biyu kuma babban abin da nake buri shi ne zuri'ata, akwai 'ya'yana, akwai 'ya'yan kannena da na abokaina da marayu ina son kafin Allah ya ɗauki rai na, ia ga cigabansu da ɗaukakarsu, idan kuma hakan bai yiwu ba, Allah ya daukaka su bayan rai na," in ji shi.