Yadda kadoji suke kai wa mutane hari a yayin da ake fama da karancin ruwa a Iran

- Marubuci, Daga Sarbas Nazari
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Kwance a kan daben cikin gidansa, Siahouk ne ke fama da tsananin radadin raunin da ke hannunsa na dama da ya samu a sakamakon gamuwa da abin firgicin da ya yi.
Kwanaki biyu kacal da suka gabata, da tsakar rana mai tsananin zafi cikin watan Agusta, wani gawurtaccen kada da ake yi wa lakabi da gando ya far wa makiyayin mai shekaru 70, yayin da ya tafi diban ruwa a wani tafki a yankin Baluchistan na kasar Iran.
"Ban taba tunanin faruwar hakan ba,'' ya tuna da mummunan al'amarin da ya faru da shi shekaru biyu da suka gabata, yayin da har yanzu mamaki da razana ke nunawa cikin idanunsa.
Siahouk ya samu kubuta ne bayan da ya samu ya samu ya yi kokarin matse wata robar ruwan sha a tsakanin mukamukinsa," ya bayyana, a yayin da yake shafa fuskarasa mai kasusuwa da hannunsa mai tamoji.
Jinin da ya zubar ya sa Siahouk ya suma har na tsawon rabin sa'a. An kuma gano shi ne bayan da garken tumakinsa suka dawo gida su kadai zuwa karamin kauyensu na Dombak.
Zamantakewa mai cike da hadari
Labarin Siahouk ya yi nuni da yadda hakan ya faru da sauran wadanda farmakin kadan ya shafa, akasari kananan yara.
Akasari, labari game da kananan yaran Baluchi da ke fama da raunuka kan kasance manyan labaran da suka fi karade kafafen yada labaran kasar Iran, amma kuma akan yi saurin mantawa da su.
A shekarar 2016, kada ya hadiye wata karamar yarinya mai shekaru tara da ake kira Alireza. Kana a watan Yukin shekarar 2019, Hawa mai shekaru 10 ta rasa hannunta na dama a harin kadan.
Yayin da take dibar ruwan wanki, sauran kadan kadan ya janye ta kafin wadanda ke tare da ita su cece ta.

Hare-haren na zuwa a daidai lokacin da kasar Iran ke fama da matsanancin karancin ruwa, ta wani gefen kuma, janyewar tafkuna da koguna sun haifar wa da gandos karancin samun abinci.
Dabobin da ke fama da yunwa na daukar mutanen da suka tunkari mazauninsu a matsayin abinci ko kuma wasu barazanar da ta haifar musu da karancin abincin.
Gandos wasu nau'in kadaoji ne masu dogon baki ne da suka yadu a fadin kasar Iran da sassan nahiyar India, da Kungiyar masu lura da gandun daji da halittu da kasa da kasa (IUCN) ke dauka a matsayin "masu fuskantar hadari."
Kasar Iran na da adadin guda 400, da suka hada da kashi 5 bisa dari na halittun. Ma'aikatar lura da muhalli ta kasar Iran ta bayyana cewa tana kokarin ganin ta yi adalci wajen lura da gando da kuma kare rayukan mutanen yankin.

Duk da wadannan munanan abubuwan da ke faruwa a cikin shekarun baya bayan nan, babu alamu sosai na cika alkawari game da shawo kan matsalar.
Yayin da kake kan hanyar bulaguro a gefen Kogin Bahu-Kalat, ba a cika ganin allon alamu na gargadi game da hadari a ainihin mazaunin gandos a kasar Iran ba.
Rashin kasancewar wani tsari daga gwamnati, yasa masu aikin sa kai suka yunkuro wajen kokarin ceto halittun ta hanyar kase musu kishirwa da yunwa.
A Bahu-Kalat, kauyen da ake lakaba wa sunan kogin a bakin titi daga Dombak, ina zaune tare da Malek-Dinar, wanda ya zauna tare da gando har na tsawon shekaru.
"Na kashe lambuna da ruwan dake kwaranyowa duk saboda wadannan halittu," ya ce, na filin da a baya ya kasance mai cike da ayaba, da lemon zaki, da mangwaro.

Kogin da ke wurin, gida ne ga wadannan kadoji da y asana ciyarwa da tsokar hakarkarin kaji, saboda '' tsananin zafi mai kisa ya sa kwadi wanda abincinsu ne, suka yi karanci."
"Ku taho nan, ko taho nan," Malek-Dinar yana ta kiran kadojin, yayin da yake kiransu daga nesa-nesa. Cikin kiftawa, guda biyu suka bullo, suna jiran a ciyar da su tsokar kazar daga cikin wani farin bokiti da suka saba gani.
'Wa zai iya rayuwa babu ruwa?'
Karancin ruwa a kasar Iran ba wani sabon abu bane a yankin Baluchistan. A cikin watan Yuli ne mummunar zanga-zanga ta barke a yankin kudu maso yammacin lardin Khuzestan mai arzikin man fetur.
Kana a karshen watan Nuwamba ne 'yan sandan kwantar da tarzoma a tsakiyar birnin Isfahan suka harba harsasan roba a kan masu zanga-zanga da suka taru a bakin Kogin Zayandeh-Roud.
A yayin da dumamar yanayi ke kara muni a kasar Iran, barazanar da yankin Baluchistan ke fuskanta ka iya kara zama mai munin gaske idan aka yi la'akari da shekarun da aka shafe na rashin tattalin ruwa.
Bayan matsawa daga Shir-Mohammad Bazar don samun matsuguni daga kura da guguwa, na hadu da wasu mata na yin wanki a waje.

"Akwai wuraren zama amma kuma babu ruwan famfo,'' Malek-Naz mai shekaru 35 ta shaida min.
Mijinta, Osman ya yi min wani irin kallo game da tambayar da na yi game da ruwan wanka, yana mai nuna wata mata da ke yi wa dan ta wanka a cikin wani mazubi mai cike da ruwa mai dandanon gishiri a kusa da su.
Osman, mai yaya biyar, da dan uwansaa Noushervan, da suka shiga cikin tattaunawar, na samun kudaden shiga daga dakon man fetur zuwa kasar Pakistan, inda ake sayarwa da tsada fiye da a gida.
"Akwai hadurra da dana,'' Noushervan ya bayyana a cikin murya mai cike da damuwa. ''Amma ba komai muddin babu wani abin yi.'' Kana hadarin a bayyane yake. A cikin watan Fabrairu ne masu jami'an tsaron kan iyakar kasar Iran suka bude wuta kan wasu masu fasa-kwaurin man fetur'', tare da hallaka 10.
Irin wannan farmakin ba sabon abu bane a yankunan kan iyakoki, inda gwamnatocin kasar Iraqi ke nuna damuwa game da harkar tsaro.

"Suna nuna halin ko in kula game da damuwarmu,'' Osman ya ce, yana mai kokawa kan abinda shi da mutanen Baluchis suka bayyana a matsayin '' watsi da al'umma da gangan''.
Har yanzu, a gare shi da sauran 'yan Baluchis da dama rashin aikin yi karamin abu ne idan aka kwatanta da karancin ruwa da ya haddasa wa gandos - ''halittu masu daraja da a baya suke zaune lafiya da su - suka juye suka zama makiyansu.
"Ba ma sa ran wani taimako daga gwamnati. Ba ma sa ran su samar mana da guraban ayyuka,'' in ji Noushervan. "Mu 'yan Baluchis za mu iya rayuwa da cin burodi a cikin hamada. Amma ruwa muhummin abu ne na rayuwa.
Ba za mu taba rayuwa baba shi ba, kuma wa taba yin haka?"












