Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Malama Tasalla Nabulusi
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Wata Malamar addinin Musulunci a jihar Kano da ke Najeriya Fatima Lawan Aliyu da ake kira Malama Tasalla Nabulusi ta ce babban ƙalubalen da ta fuskanta shi ne na ƙarancin ilimin mata a jihar kano wanda ya zama gwagwarmaya a gare ta kuma gwagwarmayar ta taimaka wajen janyo hankalin mata waɗanda ba musulmi ba zuwa ga addinin.
Malamar ta shaidawa filin Ku San Malamanku cewa tun tana shekara 18 take karantarwa a Islamiyya, kuma matasalolin da ta ci karo da su sun haɗa da yadda wasu mazan da ke hana matansu zuwa neman ilimi.
ta ce babban abin da ta sa a gaba shi ne tabbatar da ganin mata sun fahimci ilimin addini tun daga tarbiya har zuwa yadda mace za ta kula da kanta da gidanta da sanin haƙƙin aure.
Malamar ta ce babban tashin hankalin da ta ji shi ne wata matar da taba zuwa ta ce ta gama haihuwa amma ba ta taɓa sanin yadda ake wankan janaba ba.
Tarihin Malama Tasalla Nabulusi
Yar asalin jihar Kano ce da aka haifa a unguwar Hausawa ta Galadanci.
Malamar ta ce ta yi karatun addini da na boko. Ta yi firamare ta unguwar Dandago.
Ta fara karatun laitattafai a wajen mahaifin mijinta har zuwa karatun Al Kur'ani da tafsirinsa
Sai dai ta ce ba ta ci gaba da karatu zuwa sakandare ba aka yi mata aure tana da shekara 14 duk da ta ci makarantar sakandare ta mata WATC.
Amma ta ci gaba da karatu inda ta yi difloma kan ilimin Hadisi da kuma babbar difloma a kwalejin ilimi ta Kano.
Kamar sauran malamai, Malama Tasalla Nabulusi ma ta ce tambayar da ta shafi matsalolin mata ne aka fi yi mata musamman aurayya da gado da rashin lafiyar mata.
Malamar ta ce ta haifi ƴaƴa 12 maza biyar da mata shida amma ɗanta na farko ya rasu
Tana da jikoki 25.
Ta ce ita kadai ce a gidan mijinta, amma ta so ya auri wata mata saboda tausayinta da ya kamata sakamakon mutuwar iyayenta da mijinta.
"Amma da muka zo sai ta ce ba ta son shi, shi kuma ya ce duk matar da ta ce ba ta son shi har abada ba ya sonta."