'Yan majalisar dokokin Ghana sun bai wa hammata iska kan haraji

Asalin hoton, Ghana parliament
Rikici ya barke tsakanin 'yan majalisa a Ghana kan kokarin gwamnati na fara karbar haraji daga masu hada-hadar kudade ta wayar salula da ake shirin kada kuri'a a kansa.
'Yan majalisar dokokin na jam'iyyar NPP mai mulki da ta 'yan adawa na jam'iyyar NDC sun bai wa hammata iska a lokacin da kakakin majalisa Joe Osei-Owusu ya tashi daga kujerarsa domin kada tasa kuri'ar ta amincewa da kudirin.
A lokacin ne 'yan adawa suka yi yunkurin hana shi saboda majalisar ta sanar da su cewa shugaban majalisar ya zama dan ba-ruwanmu a mataki irin wannan.
Yayin da aka fara kada kuri'ar karkashin wani kudiri na gaggawa, 'yan majalisa marasa rinjaye sun sha alwashin ba za su amince shugaban ya jefa kuri'arsa ba.
Wani bidiyo da ya yi ta wadari a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda 'yan majalisar suka yi ta bai wa hammata iska, suna tsallakawa domin hana Mista Osei-Owusu zuwa wurin kada kuri'ar.
Shin mece ce dokar da ta janyo ce-ce-ku-ce?

Asalin hoton, Ghana parliament
Wani sabon haraji ne da gwamnatin Ghana ke kokarin kakaba wa 'yan kasar masu hada-hadar kudade ta wayar salula - ko da intanet ko babu.
Ministan Kudin Ghana, Ken Ofori-Atta, ya yi bayani kan sabon haraji a cikin wata sanarwar kasafin kudin 2022.
Gwamnati ta gabatar da harajin kashi 1 da digo 7 kan kudin da ya haura Cedi 100 da aka yi hada-hadar su ta wayar salula.
Sai dai yawancin 'yan Ghana sun yi watsi da wannan batu, suna cewa za a kara matsawa marasa karfi a kasar shiga halin kaka-ni-kayi.
Yayin da su ma 'yan majalisa bangaren marasa rinjaye, suka marawa 'yan kasa baya, don haka suka yi watsi da kasafin kudin badin.
Sai dai daga bisani, bangaren masu rinjaye a majalisar sun amince da kasafin kudin, bayan shugaban majalisar Mista Joe Osei-Owusu, ya yi balaguro saboda rashin lafiya.
Duk da hakan, 'yan majalisar sun nuna rashin amincewa da matakin wanda karkashin dokokin majalisar ya amince a kada kuri'a.
Idan har ana son ganin dokar ta zama halattacciya, dole sai an kada kuri'a daga dukkan 'yan majalisar, wannan lamari ne kuma ya janyo dambatawar a kokarin hana shugaban majalisa fara kada kuri'ar da za ta bude hanya ga sauran mambobin majalisar.









