MDD na bukatar sama da dala biliyan 41 don aikin jinkai a kasashe matalauta

Asalin hoton, WFP
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a samar mata da dala miliyan dubu 41, yawan kudin da ba ta taba nema ba da ya kai haka domin tafiyar da ayyukanta na jin-kai a shekara mai kamawa.
Majalisar ta yi kiyasin cewa mutum miliyan 274 ne za su bukaci tallafin gaggawa a shekarar ta 2022, wato karin kashi 17 cikin dari kenan a kan na shekarar nan mai karewa.
Yayin da suke kaddamar da asusun neman kudin a Geneva, jami'an Maalisar Dinkin Duniyar sun ce rikice-rikice da aka dade ana ta yi, da kuma matsalar dumamar yanayi na ci gaba da jefa rayuwar mutanen da suka fi rauni cikin mawuyacin hali matuka gaya.

Asalin hoton, Getty Images
Tashe-tashen hankali da aka dade ana yi a kasashen Afghanistan da Yemen da kuma Syria, hadi da sabbin da ake yi a Habasha wato Ethiopia su ne suke kara yawan bukatun.
Haka ita ma matsalar dumamar yanayi kamar yadda bayanan Majalisar ta Dinkin Duniya suka nuna, tana kara raba mutane da muhallansu.
Ga kasashe masu arziki wadanda suke dari-darin bayar da kudi ga abin da suke gani kamar bukatar da ba ta karewa ta jin-kai, Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa dala miliyan dubu 41 ba ta ma kai ko kusa da abin da kasashen da suka ci gaba suka kashe ba wajen tallafa wa tattalin arzikinsu a lokacin annobar korona.
Majalisar ta ce daya daga cikin manyan matsalolin da ake fargaba a kansu a shekara mai zuwa ita ce matsalar karancin abinci, saboda tuni mutane miliyan 45 a kasashe 43 suna cikin kamfar abinci.

Asalin hoton, Others
Yanayin sabuwar shekarar da za a shiga ya tasananta fiye da na shekara mai ban-kwana, wadda a baya hukumar kula da shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita ce mafi tsanani, inda aka samu kiyasin mutane miliyan 957 wadanda ba su da wadataccen abinci a kasashe 93.
Daga cikin adadin kuma aka yi kiyasin cewa mutane miliyan 239 na bukatar agajin gaggawa a shekarar ta 2021.
Majalisar Dinkin Duniya dai ba ta samun kudaden da take bukata kashi dari bisa dari, wanda wannanan abu ne da hukumomin Majalisar suka sani farin sani, cewa ba za su samu wadannan kudade ba gaba daya.
Amman dai suna sa ran samun abin da akalla zai wadata su magance matsalar da ake fuskanta ta yunwar da ba a taba fadawa ciki ba a duniya.











