Ole Gunnar Solskjaer: Manchester United ta kori kocinta

Labari da dumi-dumi
An wallafa

Manchester United ta kori Ole Gunnar Solskjaer bayan kulob ɗin ya sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 a ranar Asabar.

Hakan ya sa Manchester United ta dawo ta bakwai a gasar Premier da maki 12 bayan Chelsea da wasanni 12 da kulob ɗin ya buga.

Sau ɗaya Manchester United ta ci wasa a league bakwai da ta buga, ciki har da kashin da Liverpool ta ba ta da 5-0 da kuma yadda da Manchester City ta lallasa ta da 2-0.

Solskjaer mai shekara 48 ya maye gurbin Mourinho a matsayin kocin wucin gadi a Disambar 2018.

Sai dai daga baya an ba kocin ɗan asalin ƙasar Norway cikakken kwantiragi a Maris din 2019 na tsawon shekara uku, inda a watan Yuli ya saka hannu a sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin zuwa 2024.

A yanzu Michael Carrick ne kulob ɗin ya zaɓa a matsayin sabon koci na wucin gadi wanda zai ci gaba da jagorantar kulob ɗin.