Abubakar Malami da wanda 'ya kai hari' gidan Mary Odili sun sa zare

Malami

Asalin hoton, Malami

An wallafa

Wata sabuwar taƙaddama ta kaure a binciken da rundunar ƴan sandan Najeriya ke yi a kan mutum 14 da ta kama, waɗanda ake zargin cewa suna da hannu a wani samame da aka kai gidan Mai Shari'a Mary Odili ta Kotun Ƙolin ƙasar.

Jagoran waɗanda ake zargin ya yi ikirarin cewa yana cikin wasu ƙwararru da suke yi wa Ministan Shari'a Abubakar Malami aiki, amma ministan ya musanta.

Rundunar ƴan sandan Najeriya kamar yadda kakakinta Frank Mba ya sanar lokacin da yake holen mutum 14 da ƴan sanda suka kama, ya bayyana Laurence Ajojo da cewar shi ne jagoran maharan, kuma sojan-gona ne da ke ikirarin cewa shi ɗan sanda ne mai muƙamin babban sufurtanda.

Ya shaida wa ƴan sanda cewa shi ƙwararre ne a harkar ƙwato kuɗi da dukiyar sata.

Duk da cewa kamar yadda ya ce shi ba ma'aikaci ba ne na sashen da ke ƙwato dukiyar sata na ma'aikatar shari'a ta gwamnatin tarayya, amma ya yi ikirarin cewa yana cikin waɗansu ƙwararru su biyar da suke yi wa Minista Malami aiki kai-tsaye.

Kuma a maganar da ake yi ma, "ministan ya ba shi aikin binciken waɗansu asussa 29, waɗanda yake aiki a kansu."

Sai dai ya ce Minista Malami ba shi da hannu a samamen da suka kai kan gidan Mai Shari'a Mary Odili.

Amma Ministan Shari'a Malami a nasa martanin, kamar yadda mai magana da yawunsa, Umar Gwandu ya fitar a cikin wata sanarwa, ya ce ba shi da wata alaƙa da Laurence Ajojo.

Sannan ya ce ikirarin da yake yi cewa yana masa aiki surkulle ne kawai, ko magana ce irin ta mai neman abokin mutuwa.

Ministan shari'ar ya ce hankali ba zai kama ikirarin Ajojo ba, idan aka yi la'akari da cewa ofishinsa yana da tarin ƙwararru da duk wani abin da ake bukata don gudanar da aikinsa.

"Don haka babu yadda zai ɗauki ɗan sandan bogi, ko wani ɗan ci-da-ƙarfi domin ya masa aiki," kamar yadda ya ce.

Mary Odili

Asalin hoton, Other

A ƙarshe dai Malami ya yi zargin cewa irin Laurence Ajojo da dangoginsa suna ƙoƙari ne su ɓata masa suna, amma ba za su yi nasara ba.

Kana ya buƙaci ƴan sanda su ci gaba da bincike har sai sun gano iyayen-gidan masu neman shafa masa kashin-kaji da dalilin da ya sa aka kai samame gidan Mai Shari'a Mary Odili.

A halin da ake ciki dai ƴan sanda sun bayyana cewa sun samu waɗansu abubuwa a gidan jagoran maharan Mista Ajojo, ciki har da kwamfuta da waɗansu katin shaida biyu na jabu - ɗaya na nuna cewa Ajoji ɗan sanda ne, ɗaya kuma na cewa ma'akacin hukumar EFCC ne.

A ranar Alhamis ne rundanar ƴan sandan Najeriya ta nuna wa duniya mutum 14 da ake zargin.

Kuma kakakin rundunar ya ce sun gano daya daga ciki yana ikirarin shi ɗan jarida ne na kamfanin Thisday, amma hukumomin jaridar sun musanta, suna cewa sun yi sallama da shi tun shekaru 15 da suka wuce.

Haka kuma akwai wani malamin tsibbu, da wasu ragowar mutum bakwai, ciki har da sojoji, waɗanda aka ce sun yi ɓatan-dabo.

A ranar 29 ga watan Oktoba ne aka kai samame gidan Mai Shari'a Mary Odili, inda aka yi ta zargin ɓangarori da dama, cewa suna da hannu a ciki.

Ciki har da hukumar tsaro ta DSS da ƴan sanda da EFCC da kuma Ministan Shari'a, amma duka sun musanta.

Karin wasu labaran masu alaƙa