Ana sukar matakin Poland na hana 'yan ci-rani daga Belarus shiga kasarta

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Poland sun ce sun dakile wani yunkuri na shigar 'yan ci-rani kasar, ta iyakarta da Belarus, tare da gargadin dubban 'yan ci-ranin da ke tafe su yi taka tsan-tsan.
Hotuna da bidiyon da aka yada a shafukan intanet, sun nuna dubban 'yan ci-ranin na kokarin tsallaka wayar da ta kewaye iyakar kasashen biyu.
Gwamnatin Poland ta kira matakin mai tayar da hankali, tare da girke jami'an tsaro 12,000 zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.
Kasar ta zargi Belarus da ingiza 'yan ci-ranin zuwa iyakarsu, tare da bayyana hakan a matsayin keta.
Kasashen Poland, da Lithuania da Latvia sun ce an samu karuwar mutanen da ke kokarin tsallakawa kasashe ba bisa ka'ida ba cikin watannin da suka gabata.
Yawancinsu kuma sun fito daga yanking Gabas ta Tsakiya, da Asiya ne.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Tarayyar Turai ma ta zargi Shugaba Alexander Lukashenko na Belarus da janyo wa 'yan kasar halin da suke ciki.
Ga tsadar rayuwa saboda jerin takunkumin da aka kakab wa kasar, dalilan da ya sa suke kokarin tserewa ta kowacce hanya.
Ita ma kasar Poland, da ake suka kan matakin korar 'yan ci-ranin da hana su shiga kasarta da take yi ta mayar da martini, inda ta kare matakin da cewa tudadar 'yan ci-ranin ta wuce ka'ida don haka suka kewaye iyakarta da waya mai tsini da kaifi, wadda ke iya raunata mutum.
Haka kuma, masu gadin iyakar Poland sun sanar da cewa da safiyar ranar Talata za su rufe iyakarta da Belarus da ke Kuznica.
Halin da 'yan ciranin ke ciki a iyakar Poland ya munana, lamarin da ya kai ga hasarar rayuka, ana kuma nuna damuwa kan tsaron rayukansu sakamakon matsanancin sanyin da ake fama da shi.
Yayin da Poland ta ki amincewa su shiga kasarta, ita kuma kasar Belarus ta ki amincewa su koma gid., 'Yan ci-ranin na tsaka-mai-wuya ta rashin sanin inda za su nufa, kasarsu ta gado da suka tserewa saboda matsin tattalin arziki da wasu wahalhalu ta rufe kofarta gare su.
Yayin da ita kuma wadda suke kallon tudun-mun-tsira ta ki amincewa su shige ta.
Wakilin BBC Paul Adams ya gana da Barwa Nusreddine Ahmed, wanda dan uwansa daya ne daga cikin 'yan gudun hijirar Iraqi da shi ma yake iyakar Poland tare da matarsa da 'ya'ya uku.
A watan da ya gabata ne ya isa babban birnin Belarus Minsk. Ya ce a halin yanzu suna fama da rashin abinci da ruwan sha a inda suke.










