Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaƙin Tigray na Ethiophia: Akwai yiwuwar gwamnati da 'yan tawaye sun aikata laifukan yaƙi - Rahoto
Dukkan ɓangarorin da ke yaƙi da juna a yankin Tigray na ƙasar Habasha wato Ethiophia sun karya dokokin kare haƙƙin ɗan Adam, waɗanda ka iya zama laifukan yaƙi kan rayuwar mutanen, a cewar wani sabon rahoto.
An samu rahotannin kisan azarɓaɓi da azabtarwa da fyaɗe a rikicin, kamar yadda rahoton ya nuna.
Wani binciken haɗin gwiwa da Hukumar Kare Haƙƙi ta Ethiophia da Ofishin Kare Haƙƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) suka gudanar ya ce akwai hujjojin da ke nuna aikata laifukan yaƙin.
Yaƙin ya ɓarke ne ranar 4 ga Nuwamban 2020.
An fara fafatawar ce lokacin da Firaministan Ethiophia Abiy Ahmed ya umarci a kai wa dakarun 'yan tawaye hari a yankin Tigray da ke arewacin ƙasar.
Dakarun gwamnati sun yi nasarar zaƙulo mayaƙan tun da farko amma lamura sun sauya a watan Yuni bayan dakarun 'yan tawayen sun fara ƙwace garuruwa. Yanzu haka rahotanni na cewa suna yunƙurin shiga Addis Ababa, babban birnin ƙasar.
A ranar Talata ne kuma gwamnati ta saka dokar ta-ɓaci 'yan awanni bayan ta shawarci mazauna birnin da su nemi makamai.
Yaƙin ya haddasa bala'o'i iri-iri. An kashe dubban mutane, an kori wasu daga muhallansu a yankin na Tigray yayin da wasu ke fuskantar yunwa.
"Akwai hujjoji a ƙasa da ke nuna cewa dukkan ɓangarori a rikicin sun kai hari...ko dai kai-tsaye kan wuraren farar hula, kamar makarantu da gidaje da asibitoci da wuraren ibada, ko kuma sun kai hare-haren da suka jawo mutuwar fararen hula ko rusa muhallansu," a cewar rahoton.
Kazalika, an samu rahoton kisa ba tare da wani dalili ba.
Rahoton ya bayyana yadda wata ƙungiyar matasa a Tigray mai suna Samri ta kashe 'yan ƙabilar Amhara 200 a Mai Kadara a watan Nuwamban da ya gabata. An dinga kai wa 'yan Tigray harin ramuwar gayya a garin.
Sojojin Eritrea sun shiga yaƙin, inda suka dinga taya na Ethiophia yaƙar 'yan tawayen na Tigray. Sojojin na Eritrea sun kashe farar hula fiye da 100 a Aksum da ke tsakiyar Tigary a Nuwamban 2020, in ji rahoton.
"Akwai yiwuwar an aikata laifukan yaƙi tun da dai akwai hujjoji cewa an kashe wasu da gangan waɗanda ba su shiga yaƙin ba," a cewar rahoton.
Kazalika, an bayyana rahotannin aikata fyaɗe da dukkan ɓangarorin suka aikata kan mata da maza da ƙananan yara maza da mata.
A ɗaya daga cikin laifukan, an tsare wata matashiya mai shekara 19 sannan aka dinga yi mata fyaɗe har tsawon wata uku. Haka nan an samu rahoton yin lalata da wata mace mai lalurar nakasa.
Rahoton ya ƙara da cewa an yi amfani da cin zarafi da lalata "da zummar ƙasƙantar da mutanen".
Hukumomin sun yi kira ga gwamnatin Ethiophia ta gudanar da "cikakken bincike ta hanyar ƙungiyoyin bincike masu zaman kansu kan zarge-zargen domin gurfanar da waɗanda suka aikata laifukan a gaban kotu".