Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Tigray: Shugaban Ethiopia Abiya ya yi kira ga 'yan kasar su dauki makamai
Firaiministan Ethiopia, Abiy Ahmed, ya yi kira ga 'yan kasar su dauki matakai domin tunkarar 'yan tawaye.
Ya yi kiran ne a shafinsa na Facebook bayan wasu rahotannin sun nuna cewa 'yan tawaye daga jihar Tigray da ke arewacin kasar sun kwace ikon garuruwa da dama da ke jihar Amhara mai makwabtaka.
Gwamnati ta zargi mayakan 'yan tawaye da kisan matasa 100 a daya daga cikin garuruwan da suka kwace.
Amurka ta yi kira a tsagaita wuta a fadan da aka kwashe shekara guda ana yi wanda ya yi sanadin raba miliyoyin jama'a daga gidajensu.
Kungiyar Tigray People's Liberation Front (TPLF) ta ce babban burinta shi ne ta kutsa kai lardin arewacin kasar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mr Abiy ya ce matsowar da 'yan tawaye suke yi zai "jefa kasar a yanayin da za ta kau daga doron kasa".
Ya yi kira ga 'yan kasar su "hada kai sannan ku yi maci bisa ka'ida tare da makamai da iko.. domin hana, da kuma wuyawa da kuma binne 'yan ta'addar TPLF", a cewar fassarar kalamansa da shafin intanet na Addis Standard ya yi.
Kalaman nasa sun zo ne a yayin da rahotanni suke cewa 'yan tawayen sun kama garuruwan Dessie da Kombolcha da ke jihar Amhara, wadanda suke da nisan kilomita 300 daga babban birnin kasar Addis Ababa.
A wani sakon Tuwita da ta wallafa ranar Litinin, gwamnatin Ethiopia ta ce 'yan tawayen "sun kashe fiye da matasa 100" a yankin Kombolcha area. Sai dai kungiyar TPLF ba ta ce komai a kan wannan zargi ba.
Yana da matukar wahala a tantance gaskiya ko rashin gaskiyar wadannan zarge-zarge na dukkan bangarorin saboda an katse hanyoyin sadarwa.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana bacin ransa kan yadda rikicin ya ki ci ya ki cinyewa. A wani sakon Tuwita, ya ce ci gaba da fadan yana kara jefa mutane cikin mawuyacin hali a arewacin Ethiopia.
An kashe dubban mutane tun daga soma rikicin, yayin da aka raba miliyoyinsu daga gidajensu kuma sun fada cikin halin matsanaciyar yunwa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.