Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin bam ya hallaka mutum tara a Yemen
Akalla mutum tara ne suka mutu, a wani harin bam da aka dasa a cikin mota a kusa da filin jirgin sama a babban birnin Yemen na wucin gadi wato, Aden.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutum 12 sun jikkata a harin da aka kai ranar Asabar wanda Firaminista Mueen Abdulmalek Saeed ya kira da na ta'addanci.
Ganau sun shaida wa BBC cewa cikin wadanda suka mutu har da mata da kananan yara, kuma kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Kafar yada labaran yankin ta ce harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan birnin Aden ke sauka filin jirgin saman, sai dai bai ji rauni ba.
Makwanni uku da suka gabata aka taba yunkurin kai wa gwamnan wani harin bam da ya tsallake rijiya da baya, amma mutum shida sun ji rauni kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.
Harin da aka kai na ranar Asabar shi ne mafi muni a Aden, baya ga wanda ya faru a watan Disambar bara da mutum 22 suka mutu.
Gwamnatin Yemen da kasashen yammacin duniya ke marawa baya dai na da mazauni ne a Aden tun shekarar 2014, lokacin da 'yan tawayen Houthi suka fatattaki dakarun gwamnati da ita kan ta gwamnatin daga birnin Sanaa tare da karbe iko da shi.
Yaki ya kara kazancewa a shekarar 2015, lokacin da kawancen kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya suka kaddamar da hare-hare kan 'yan Houthi, tare da marawa shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi baya.
Tashin hankalin da Yemen ta samu kann ta a ciki ya janyo sanadin mutuwar sama da mutum 110,000, tare da janyo aikin agaji mafi mafi muni a duniya, inda miliyoyin 'yan kasar suke fama da matsananciyar yunwa, wasu sun yi gudun hijira.
A bangare guda kuma tashin hankalin ya kara munanan lamarin barkewar annobar cutar korona, inda ake fama da karancin kayan aiki, da magunguna da wuraren ajiye marasa lafiya sai uwa uba durkushewar tattalin arziki.