Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: An raba maki tsakanin Brazil da Moroko

Takaitaccen Bayanin Wasa

Brazil 1 , Morocco 1 at Full time
Brazil
Moroko
Full time
Hutun rabin lokaci Brazil 1 , Moroko 1

Key Events

Brazil

  • Vinícius Júnior Goal 32 minutes

Moroko

  • I. Saibari Goal 21 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Brazil,Bruno Guimarães (32 minutes)
Moroko,B. Díaz (21 minutes)

Taƙaitattu

  • Brazil za ta fafata da Morocco a rukuni na uku a gasar cin kofin duniya
  • Wannan shi ne karo na 23 da Brazil ke zuwa kofin duniya mai biyar jimilla
  • Morocco za ta buga gasar kofin duniya na bakwai, ta kai daf da karshe a 2022
  • Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
  • Za a buga wasan ne a filin MetLife da ke New Jersey a birnin New York
  • Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
  • Scotland da Haiti suma suna cikin rukunin na uku a gasar kofin duniya 2026
  • Kasa 10 ce daga Afirka da za su buga gasar kofin duniya a bana
  • Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp

Rahoto kai-tsaye

Mai gabatarwa Mohammed Abdu da taimakon AI

  1. A nan muka kawo karshen shirin

    A nan muka kawo muku karshen shirin da fatan za ku tara a sauran wasannin gasar cin kofin duniya 2026 da za mu ke kawo muku kai tsaye.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada nake muku asuba ta gari.

  2. Wasannin da za a buga ranar Lahadi a gasar kofin duniya 2026

  3. Yadda aka gara ƙwallo tsakanin kasashen biyu

  4. An tashi daga wasan sun raba maki a tsakaninsu, Brazil 1-1 Moroco

    An tashi wasan farko a rukuni na uku da ci 1-1.

    Moroko mai wakiltar Afirka ta samu maki ɗaya a wasan farko.

    Afirka ta Kudu kuwa ta yi rashin nasara a hannun Mexico a wasan farko.

    Saura kasa takwas daga Afirka daga 10 da za su wakilci Afirka su buga wasanninsu.

  5. , Brazil 1-1 Morocco

    Har munci minti bitar daga goma da aka kara, saura biyar a tashi daga karawar.

    Kamar dai tawagogin biyu sun gamsu da raba maki a wannan karawar.

  6. , Brazil 1-1 Morocco

    Fabinho ya yi keta koda yake daga tsakiyar fili ne, kuma ba a bashi katin gargaɗi ba mai ruwan ɗorawa.

  7. , Brazil 1-1 Morocco

    An samu bugun kusurwa daga Moroko ta kuma buga, amma dai ba ta amfana da wannnan damar ba, ƙwallo ta fita jifa gidan Brazil.

  8. , Brazil 1-1 Morocco

    An samu bugun kusurwa da Brazl ta yi ta wajen Cunha, amma babu hatsari Moroko ta fitar da ƙwallon ba wata matsala.

  9. , Brazil 1-1 Morocco

    An yi karin minti 10, Kda ka je ko ina, domin komai zai iya faruwa a cikin minti 10 a wasan tamaula.

  10. , Brazil 1-1 Morocco

    Yassine Bounou ya ci gaba da tsare ragar Morocco, duk da ɗan ciwo da ya ji a kafaɗa, kuma yanzu lokaci ya ja sosai.

  11. Brazil ta yi canji na karshe na biyar, Brazil 1-1 Morocco

    Carlo Ancelotti ya canja ɗan wasa na biyar a karawar, inda Danilo Santos, wanda ya taka leda shekara biyu tare da Nottingham Forest ya canji Bruno Guimaraes na Newcastle.

  12. , Brazil 1-1 Morocco

    Raphinha ya buga kwallon zuwa ga Vinicius Jr daga kusa da gefen layi, amma Yassine Bounou na kwallon Morocco ya fahimci abin da ake son yi ya fito ya samu ƙwallon..

  13. , Brazil 1-1 Morocco

    Chemsdine Talbi ya buga ƙwallo da kafar dama, amma babu wani ɗan Moroko da zai ɗauka.

  14. , Brazil 1-1 Morocco

    An sanar da waɗanda suka shiga filin wasa a karawar Brazil da Morocco sun kai 80,663.

    Shin za su iya ganin wadda za ta haɗa maki a karawar nan ko kuma haka za su tashi?

  15. , Brazil 1-1 Morocco

    Yanzu dai Moroko ne suka yi bani in baka tun daga gurbin masu tsaron baya ana wani gudu da ƙwallo har kusa da ragar Brazil, daga karshe an fitar da ƙwallon ba wani haɗari.

  16. , Brazil 1-1 Morocco

    An buga kwallon daga can gefe ta wuce ta cikin gidan Moroko, amma babu wani ɗan Brazil da ya kamata ya yi wani abu, kenan ƙwallon ya yi faɗi.

  17. An je ɗan karamin hutun shan ruwa

    A wannan lokacin ana fuskantar yanayi mai zafi a Amurka, hakan ya sa ya zama wajibi alkalin wasa ya bayar da damar aje a sha ruwa a hutu a goge gumi, sannan a ci gaba da taka leda.

  18. Moroko ta yi canji, Brazil 1-1 Morocco

    Fabinho ya ji rauni a lokacin da aka bugi bakinsa, yana da kyau ya je a duba lafiyarsa.

    Morocco ta yi canja ƴan wasa biyu, inda Azzedine Ounahi da Bilial El Khannouss suka maye gurbin mai taka leda a Sunderland, Chemsdine Talbi da kuma Samir El Mourabet mai shekara 20, wanda ke taka leda a Faransa tare da Strasbourg.

  19. Brazil ta kara yin canji na huɗu kenan kawo yanzu, Brazil 1-1 Morocco

    Wannan shi ne canji na huɗu daga biyar da Carlo Ancelotti ya sauya ƴan wasa kawo yanzu. An canja Igor Thiago an maye gurbinsa da Matheus Cunha na Manchester United.

    Saura canji ɗaya ya rage wa Brazil

  20. , Brazil 1-1 Morocco

    Dukkansu tawagogin na neman kara cin ƙwallo, amma babu wata dama da aka samu, kuma a zagaye na biyu Brazil ta fi dannawa, amma kuma babu wani kalubale daga Moroko.

    Watakila sun gamsu da wannan sakamakon 1-1, domin babu wanda ya yunkura ya kara cin ƙwallo, amma an fi gara leda a gidan Moroko.