'Yar fim da ake tuhuma da rashin kamun kai a Yemen

An wallafa

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce tuhumar da gwamnatin Yemen take yi wa wata 'yar fim mai tallan kayan kawa bisa "rashin kamun kai" da mallakar kwayoyi rashin adalci ne.

Dakarun Houthi da ke birnin Sanaa suke tsare Intisar al-Hammadi, mai shekara 20, wadda ta musanta zargin, a watan Fabrairu.

An doki lauyanta sannan aka riƙa zaginsa, kana aka tilasta masa sanya hannu kan wasu takardu bayan an rufe masa idanu.

Kazalika masu shigar da kara sun yi barazanar tilasta mata yin "gwajin budurci".

Lauyanta ya shadai wa HRW cewa an hana shi ganin takardun karar Ms Hammadi kuma an hana shi wakiltarta lokacin da ta gurfana a gaban kotu sau biyu a farkon watan nan.

Mayakan Houthi, wadanda suka dade suna fafatawa da gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka yarda da ita tun a 2015, ba su ce komai a kan batun ba.

Ms Hammadi, wadda mahaifinta dan kasar Yemen ne yayin da mahaifiyarta 'yar Ethiopia ce, ta kwashe shekaru hudu tana aiki a matsayin mai tallan kayan kawa sannan ta fito a fina-finan Yemen biyu da ake yi zango-zango.

A wasu lokutan kan wallafa hotunanta a shafukan intanet ba tare da dankwali ba, abin da ya ci karo da dokokin kasar.

Lauyanta ya ce tana cikin mota ita da wasu mutum uku a kan hanyarsu ta zuwa Sanaa ranar 20 ga watan Fabrairu lokacin da dakarun 'yan tawayen Houthi suka tsayar da su, sannan suka kama su.

An rufe fuskar Ms Hammadi sannan aka tafi da ita ofishin 'yan sanda da ke bincike kan manyan laifuka, kuma aka tsare ta tsawon kwana 10.

"An ƙwace wayarta da kuma hotunanta na tallan kayan ƙawa inda aka ce suna yada rashin ɗa'a don haka ita karuwa ce [a cewar hukumomin Houthi]," a cewar lauyan a hirarsa da HRW.

A cewar HRW, an shaida wa kungiyoyin kare hakkin dan adam da lauyoyi da aka bari suka gaba Ms Hammadi a gidan yari a watan Mayu cewa an tilasta mata sanya hannu kan wasu takardu idonta a rufe.

Bayanai sun nuna cewa takardun na nuna cewa "ta amince" da aikata laifukan da ake zarginta a kansu.

A watan Maris, an dauke Ms Hammadi zuwa Babban Gidan Yarin Sanaa, inda masu gadinsa suka rika kiranta "karuwa" kuma "baiwa", saboda bakar fatarta da kuma asalinta na kasancewa mai tsatson Ethiopia, in ji lauyanta.

Ya kara da cewa masu shigar da kara sun dakatar da shirinsu na tilasta mata yin "gwajin budurci" a farkon watan Mayu bayan Amnesty International ta fitar da rahoton da ya yi alla-wadai da hakan.