A karon farko an ci Real Madrid a gasar La Liga ta bana

An wallafa

Espanyol ta doke Real Madrid da ci 2-1 a wasan mako na takwas a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Raul De Tomas ne ya fara ci wa Espanyol kwallo minti na 17 da fara tamaula, sannan Aleix Vidal ya kara na biyu a zagaye na biyu.

Real ta zare kwallo daya ne ta hannun Karim Benzema saura minti tara a tashi daga fafatawar, kawo yanzu dan wasan tawagar Faransa ya ci 10 a kakar bana kenan.

A kakar bara da suka fafata a La Liga, kungiyar Bernabeu ce ta doke Espanyol gida da waje, inda ta ci 2-0 ranar 7 ga watan Disambar 2019, sannan ta ci 1-0 a gidan Espanyol ranar 28 ga watan Junin 2020.

Real din tana nan a matakinta na daya da maki 17, bayan cin wasa biyar da canjaras biyu da rashin nasara daya.

Atletico Madrid wadda ta yi nasara a kan Barcelona da ci 2-0 ranar Asabar, ita ce ta biyu da maki 17 iri daya da na Real Madrid.

Barcelona mai kwantan wasa tana da maki 12, wadda ta yi nasara a karawa uku da canjaras uku da rshin nasara a wasa daya.

Espanyol tana ta 12 a teburin kakar bana da maki tara, bayan yin nasara a fafatawa biyu da canjaras uku aka doke ta wasa uku.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao ranar Lahadi 17 ga watan Okroba a fafatawar mako na tara.

Ita kuwa Cadiz za ta ziyarci Espanyol ranar Litinin 18 ga watan Oktoban, yayin da Barcelona za ta kara da Valencia ranar Laahadi 17 ga watan Oktoban a Nou Camp.