Conte na son ya gaji Ole a United, Arteta ya ce Lacazette ba na sayarwa bane

Antonio Conte
An wallafa

Tsohon kocin Juventus da Chelsea da kuma Inter Milan, Antonio Conte na sha'awar horar da Manchester United idan kungiyar da ke buga Premier League ta kori Ole Gunnar Solskjaer. (The Transfer Window Podcast via Star)

Everton na shirin taya dan wasan Chile da Inter Milan, Alexis Sanchez, bayan da tsohon dan kwallon Arsenal da Manchester United zai iya barin kungiyar Italiya a watan Janairu.

Dan kwallon tawagar Netherlands da Manchester United, Donny van de Beek ya bukaci wakilinsa da cewar ya tuntubi Real Madrid ko za ta dauke shi. (Sun)

Chelsea ba za ta biya kunshin kwantiragin fam miliyan ta dan wasan Atletico Madrid, Saul Niguez domin ta mallake shi ba. Dan kasar Sifaniya ya kasa taka rawar gani tun bayan da ya koma buga wasannin aro a Stamford Bridge a watan Agusta. (La Razon - in Spanish)

Watakila mai tsaron bayan tawagar Ingila, Chris Smalling yana daga cikin 'yan wasan Roma da yawa da za su bar kungiyar a watan Janairu. (Calciomercato - in Italian)

Chris Smalling

Asalin hoton, Getty Images

Matashin dan wasan tawagar Faransa mai taka leda a Leicester City, Wesley Fofana na daga cikin wanda Manchester United da kuma Newcastle ke son yin zawarci. (Sport Witness)

Kocin Arsenal, Mikel Arteta ba zai sammala duk wani tayi da za a yi wa Alexandre Lacazette don barin Gunners a watan Janairu, maimakon haka za su jira kwantiraginsa ya kare a karshen kakar bana, domin ya bar Emirates ba tare da yarjejeniya ba. (Sun)

Real Madrid da Bayern Munich na kara matsa kaimi domin sayen dan kwallon Jamus Antonio Rudiger, wanda bai cimma matsaya tatsawaita zamansa a Stamford Bridge ba. (ESPN)

Abin da ke gaban Rudiger shine ya ci gaba da taka leda a Chelsea, sai dai a shirye yake da duk wadda za ta taya shi da tsoka. (Fabrizio Romano)

Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City da Tottenham da Liverpool da kuma Newcastle na rubibin sayen Ousmane Dembele, wanda watakila ya bar Barcelona a karshen kakar bana. (90Min)

Kyaftin din Newcastle United, Jamaal Lascelles ya ce ya kamata 'yan wasan kungiyar su dauki alhakin laifin korar Steve Bruce da aka yi. (Mail)

Manchester City za ta bi sahun Barcelona wajen rige-rigen daukar dan kwallon Ajax, Antony. (El Nacional - in Spanish)

West Ham da kuma Southampton na son daukar dan kwallon Sassuolo, Filip Djuricic, wanda ya buga wasannin aro a Southampton a kakar 2014-15. (Calciomercato - in Italian)